✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi wa matar aure fyaden gandu

’Yan bindigar sun yi ta yi wata matar auren fyaden gandu har ta galabaita.

Wasu ’yan bindiga su biyar sun yi awon gaba da wata matar aure, suka kuma yi mata fyaden taron dangi har sai da ta fita daga hayyacinta.

Gungun ’yan bindigar sun kama matar ne a ranar Alhamis a kauyen Suna da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Matar ta baro sansanin ’yan gudun hijira da ke Zumba ne da nufin zuwa ta gida ta kwaso kayan abinci a kauyen Suna, amma ta yi gamo da ’yan bindigar da suka tisa keyarta zuwa cikin daji suna mata fyade daya bayan daya har sai da ta fadi ranga-ranga.

Daga baya aka tsinci gawata a cikin jejin, aka dauko ta zuwa Babban Asibitin Minna, inda a halin yanzu ake jinyarta.