✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindigar da suka kashe masallata a Neja sun shiga hannu

Mutum shida daga cikin wanda suka kashe masallatan sun shiga hannu.

Akalla mutum shida ne da ake zargi da hannu a kisan wasu masallata 18 a yankin Maza-Kuka a Karamar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, suka shiga hannun jami’an tsaro.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkar Tsaron Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, ne ya bayyana hakan a birnin Minna a ranar Laraba.

Sai dai ya ce bai san hakikanin adadin wanda aka kama ba, amma da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun,ya bayyana mutum shida aka kama.

A cewarsa “Binciken ’yan sanda ya gano shugabansu da yaransa na daga cikin wanda suka tsere daga gidan yarin garin Lokoja.

“Yayin da ragowar kuma aka same su da laifin safarar makamai da miyagun kwayoyi.”

Kazalika, Kwamishinan ya ce Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello, ya sanya sabuwar dokar ba wa ’yan banga dama don karfafa harkar tsaro a jihar.

Umar ya bayyana yadda ’yan bindiga ke azabtar da wasu yankunan Jihar ta hanyar karbar haraji kafin su samu damar yin noma a gonakinsu.

Ya ce Gwamnatin Jihar na iya bakin kokarinta wajen ganin ta hada kai da duk wasu masu bukatar sa kai wajen dakile ayyukan mahara, tare da tabbatuwar tsaro a fadin Jihar.

“Muna kokarin hada kai da duk wanda za su taimaka wajen samun tsaro. Don haka, nan gaba babu wani manomin da zai bayar da wani abu ga ’yan bindiga. Muna kira ga manoma da su ci gaba da yin noma saboda shi ne baiwar da Allah ya ba su. Muna ba su shawara da kada su bawa bata-gari kofar canja musu rayuwa,” a cewarsa.

Umar ya ce za a bawa dukkanin ’yan sa kan da ke bukatar tallafa wa tsaro a Jihar horo, don sanin makamar aiki.