✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan bindigar da suka sace masu ibada 66 a Kaduna sun kashe 2 daga cikinsu

Shugaban CAN na Kaduna, Rabaran Joseph Hayab ne ya tabbatar da hakan.

An harbe har lahira mutum biyu daga cikin masu ibada 66 da ’yan bindiga suka sace daga cocin Emmanuel Baptist da ke Kakau-Daji a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kimanin mako daya da ya wuce ne ’yan bindigar suka mamaye cocin, inda suka kashe mutum daya sannan suka tafi da wasu da dama.

A ranar Juma’a, wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa masu garkuwar sun bukaci a basu buhunan shinkafa da galan-galan na man gyada don su sami abincin ciyar da mutanen.

Rahotanni sun ce sun bukaci iyalan mutanen su gaggauta kawo kayan da suka bukata matukar suna son tserar da rayuwar ’yan uwan nasu.

To sai dai a ranar Asabar, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, ya ce masu garkuwar sun kashe mutum biyu daga cikin wadanda suka sace din.

“A ranar Asabar, shida ga watan Nuwamban 2021, sun bude wuta akan mutum biyar daga cikinsu, biyu daga ciki sun mutu nan take, uku kuma sun ji munanan raunuka, kuma yanzu haka suna asibiti,” inji Rabaran Hayab.