✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindigar da suka sace ’yan makarantar Yawuri sun fitar da hotunansu

Daya daga cikin malaman makarantar ya tabbatar da sahihancin hotunan.

’Yan bindigar da suka sace dalibai da malamai a Kwaleji Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yawuri a Jihar Kebbi sun fitar da hotunan wasu daga cikinsu.

Dalibai da dama ne da har yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba da kuma malamai hudu ne ’yan bindigar suka sace daga makarantar bayan sun ci galaba kan masu gadinta a makon da ya gabata.

Daga bisani dai sojoji sun ce sun kwato wasu daga cikin daliban bayan musayar wuta da ’yan bindigar.

Gwamnan Jihar ta Kebbi, Atiku Bagudu dai ya tabbatar wa da iyayen daliban cewa gwamnatinsa na iya bakin kokarinta wajen ganin ta kubutar da su.

Daya daga cikin malaman makarantar da bai amince a ambaci sunansa ba ya tabbatar wa da Aminiya ranar Litinin cewa hotunan na ’yan makarantar ne.

Ga wasu daga cikin hotunan:

Wasu daga cikin daliban na Yawuri da aka fitar da hutunansu.
Wasu daga cikin daliban na Yawuri.