✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindigar Neja sun kara kudin fasar daliban Islamiyya

Masu garkuwar na barazanar kashe yaran idan aba a biya Naira miliyan 200 ba.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai 156 a makarantar Islamiyyar a Jihar Neja sun kara yawan kudin fansar da suke nema zuwa Naira miliyan 200.

’Yan bindigar sun ce sun daga kudin fansar da suka nema ne saboda iyayen daliban sun gaza biyan Naira miliyan 110 da suka nema a kan lokaci.

Bayan sanar da iyayen yaran cewa sun kara kudin zuwa Naira miliyan 200, masu garkuwar sun yi barazanar kashe su idan ba a kawo kudaden ba a kan lokaci.

Zuwa ranar Juma’a iyayen daliban na Makarantar Islamiyyar ta Salihu Tanko sun hada Naira miliyan 11 domin biyan kudin fansar daliban da aka sace a garin Tegina na Karamar Hukumar Rafi ta Jihar.

Da farko masu garkuwar sun bukaci iyayen daliban da mai makarantar da su biya kudin fansa Naira miliyan 110, idan ba haka ba za su kashe yaran, amma aka kasa tara kudaden da suka nema.

Daya daga cikin iyayen, wanda ’ya’yansa biyar ke cikin daliban da aka yi awon gaba da su su ya tabbatar cewa maharan sun kara yawan kudaden da suke bukata.

Malam Ali Muhammed wanda direban tifa ne, ya ce, “’Yan bindigar da gaske suke yi cewa za su kashe yaran idan ba a biya kudaden ba; Mu  kuma talakawa ne, muna rokon gwamnati ta taimaka mana”.

Hadiza Hashimu, wata uwa ce da ’ya’yanta biyar ke cikin daliban da aka sace ta bayyana halin da take ciki a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Ta ce tana cikin gidanta tana jin duk abin da ya faru lokacin da ’yan bindigar suke garkuwa da yaran, amma babu abin da za ta iya yi.

Biyu daga cikin ’ya’yanta masu shekaru biyu da hudu na cikin kananan yara 11 da aka sako saboda karancin shekarunsu; amma sauran ’ya’yan nata masu shekaru shida da tara da kuma 13, har yanzu suna hannun ’yan bindigar.

Ta ce har yanzu karamin danta mai shekara biyu a cikin firgici yake, duk lokacin da ya ji kara sai ya yi ta ihu cewa za a sake zuwa a kashe shi.

Wasu daga cikin iyayen daliban sun yi zargin Gwamnatin Jihar Neja da yin watsi da su.

Tun da aka sace daliban, gwamnatin ba ta ziyarci iyayen ko ta tura wakilai domin jajanta musu ba, ko yi musu bayanin kokarin da take yi na kubutar da yaran.