✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 20 a Katsina

Masu garkuwar sun harbe direban motar suka jefar da shi a jeji

Masu garkuwa da mutane sun sace matafiya 20 a kan hanyar Jibia zuwa Gurbi a Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun tare motar mutanen ne sannan suka tisa keyarsu zuwa inda aba a sani ba tun ranar Lahadi.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun harbi direban motar bayan ya yi yunkurin tserewa a lokacin da ’yan bindigar ke kokarin shiga da su cikin daji.

Ya ce masu garkuwar jefar sun jefar da shi direban motar a wurin, wanda sai bayan kwana biyu wasu kauyawa da suka je neman ice suka tsince shi.

Direban da ya tsiran da ke samun kulawa a asibiti ne ya sanar da cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba a mutum 20 zuwa cikin jejin.