✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sama da 70 sun nitse a ruwa bayan harin sojoji ta sama a Borno

Harin na zuwa ne bayan kashe 'yan Boko Haram fiye da 20

’Yan ta’addan Boko Haram sama da 70 sun nitse a wani kogi bayan wani harin da dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai suka kai musu ta sama a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna ko gabanin wannan farmakin ma, sojojin sun kai wani hari tare da hadin gwiwar rundunar tsaron fararen hula ta CJTF, inda suka kashe ’yan Boko Haram sama da 20 a kauyen Shehuri da ke karamar hukumar Bama a jihar ta Borno ranar Alhamis.

Majiyoyi daga yankin sun ce bayan harin na Shehuri, ’yan ta’addan da ke kokarin tserewa sun nitse a wani kogi da ke kusa da kauyen Dipchari a karamar hukumar Bama, ranar Juma’a.

“’Yan ta’addan sun kwashi kashinsu a hannu; sun rasa sama da mayaka 70 a kusa da kauyen Dipchari. Yanzu haka ma ana kan gano wasu gawarwakin nasu,” inji wata majiya daga jami’an tsaro.

Ita ma wata majiya da take yankin, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce bayan faruwar lamarin, an ga ’yan ta’addan na ta kokarin tsamo gawarwakin ’yan uwan nasu daga kogin.

A cewar majiyar, “Yau da safe wajen misalin karfe 8:30 na safe, sun yi jana’izar mayakan da suka nitse su sama da 50 a kauyen Dipchari, sannan suna ci gaba da neman ragowar gawarwakin.

“Sun tsamo wasu da dama, amma har yanzu akwai wasu da ba a gano ba,” inji majiyar.

Kodayake har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa daga sojoji a kan haka a hukumance, amma majiyoyi da dama daga yankin sun tabbatar da faruwar harin.

A ’yan kwanakin nan dai, sojoji suna samun gagarumar nasara a yakin da suke yi da ’yan ta’adda, musamman a yankin Arewa maso Gabas.