✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun kone gidaje da rumbunan abinci a Borno

'Yan banga sun yi nasarar dakile sake kai wani harin.

’Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari kauyen Jibwiwi na Karamar Hukumar Hawul a Jihar Borno, inda suka kone gidaje da yawa da rumbunan adana abinci.

Aminiya ta gano cewa ’yan ta’addan da suka yi wa kauyen tsinke a kan babura sun kai harin ne da misalin karfe 6:00 na yammacin Litinin.

Wani dan banga a kauyen ya ce “Sun kone gidaje takwas da wani wajen ajiye kayan abinci; wanda da yawa masara, dawa da gyada aka ajiye a cikinsa.

“Daga nan sai suka wuce yankin Ngulde da ke Karamar Hukumar Askira, amma mun dakile su tare da taimakon mafarauta.

“Kai daukin da ’yan banga suka yi ya taimaka da a can ma barna mai tarin yawa za su yi,” inji shi.

Shugaban ’yan bangar yankin Arewa Maso Gabas, Shawulu Yohanna, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce sun dakile su don kada su sake kai wani hari wani yankin.