’Yan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojoji a Yobe | Aminiya

’Yan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojoji a Yobe

    Sagir Kano Saleh

Sojoji sun ragargaji mayakan kungiyar Boko Haram da suka yi yunkurin satar jiki su shiga garin Babangida da ke Jihar Yobe a ranar Laraba.

Tawagar mayakan na Boko Haram da takwarorinsu na kungiyar ISWAP sun kwashi kashinsu a hannu ne a lokacin da dakarun Rundunar Operation Hadin Kai suka yi musu luguden wuta babu kakkautawa.

Daraktan Yada Labaran Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya ce mayakan sun cika bujensu da iska sun bar bindigarsu ta harbin jirgin sama da bindigogi kirar AK-47 da motarsu.

Nwachukwu ya ce ’yan ta’addar da yanzu lagonsu ya karye saboda matsin da sojoji suka yi musu, sun yi yunkurin su saci jiki su shiga garin ne lokacin da sojojin suka yi arba da su.

“Yanzu haka, sojojin da suka samu jinjina daga Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, saboda saurin da suka yi wajen dakile harin, suna ci gaba da bin maharan, su gama da su,” inji sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

Ya bukaci sojojin su ci gaba da ragargaza miyagun domin samar da natsuwa da aminci ga mutanen Jihar.