✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun yi wa ’yan jari-bola 20 yankan rago a Borno

Sun yi musu yankan ragon ne bayan sun harbe su da bindiga

Wasu maharan da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram /ISWAP ne sun halaka wasu masu sanaar tarawa da sayar da tsoffin karafa da akewa lakabi da ’yan Ajakuta ko yan jari-bola su kimanin 20 a garin Dikwa da ke Jihar Borno.

Wata majiya ta ce wasu mazauna garin sun bar sansaninsu na yau da kullun da ke kewayen kauyensu inda suka bi tazarar kilomita da dama bayan yankin da aka tanada don yin fatali da kayan karafa, sai kawai suka ci karo da ’yan tada kayar baya wadanda su ma suke taruwa don neman kudi.

Wasu majiyoyin rundunar tsaro ta civilian JTF sun yi ikirarin samu tattara gawarwaki kusan kuma 20 nan take suka garzaya wurin da aka kai harin inda suka gano cewar adadin ya kai 25, kuma dukkansu sun mutu ne ta hanyar harbe-harbe da aka yi a kusa da wajen da kuma ta hanyar yankan rago.

A cewar majiyar, an yi wa wadannan mutane masu fasa karafa kisan gilla ne a kauyen Boboshe Mukdala na Dikwa.

Wani mazaunin garin da ya tsira daga harin ya ce, “Maganar da nake yi da ku, mun kwashe gawarwaki 25 daga wurin wadanda aka harbe su gaba daya. Kamar dai yadda muka gano gawarwaki kimanin 20 da kuma tarkacen karafa daga inda aka kai harin.

“Mun samu wasu da raunukan harsashi. Sai da muka garzaya da su babban asibitin garin Dikwa tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya domin ceton rayukansu,” inji majiyar.”

“A bayyane yake cewa bayan sun harbe su, sun yi musu yankan rago. Akwai yara a cikinsu, Boko Haram kafirai ne,” inji shi.

Shi ma wani malamin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, maharan sun zo ne a kan babura uku kowanne dauke da mutum uku sannan suka kewaye su da manyan bindigu kafin su fara harbe-harbe.

“Sun bude mana wuta inda suka kashe kusan dukkan abokan aikina da ke wurin tare da kwashe tarkacen da aka fi sani da Ajaokuta,” inji shi.”

Da yake mayar da martani kan lamarin, wani Kwamandan sojan da ke yaki da Boko Haram, Manjo Janar Chris Musa ya bayyana kashe-kashen a matsayin mummunan abin ki.

Ya kuma ce, “Mun aika da sojoji domin su taimaka wa mutanen yankin wajen debo gawarwakin. Mun sami gawarwaki 20 a ranar, amma tun farko ‘yan Ajakutan an ba su iyaka da kada su ketare don kare lafiyar su.

Amma galibi suna shiga cikin dazuzzuka inda suke haduwa da masu tayar da kayar baya suma suna kwashe karafa abin da ya faru yayin da suka hadu da su ke nan, su kuma suka kashe su yayin da wasu daga cikin su Allah ya ba su dama suka tsere.” inji Kwamandan.