✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan canjin Adamawa sun fara gudun Dalar Amurka saboda tsoron faduwarta

“Ko a ranar Lahadi ma da na sami mai saye, sai aka yi mun mugun tayin da na gwammace na mayar da ita gida.”

’Yan canji a jihar Adamawa sun fara kin karbar wasu kudaden kasashen waje, musamman Dalar Amurka saboda rashin tabbas din farashinsu a ’yan kwanakin nan.

Wasu daga cikin masu canjin da Aminiya ta zanta da su a kasuwar Jimeta da ke Yola, babban birnin jihar, sun ce suna dari-darin karbar kudaden ne saboda fargabar yadda Dalar take karyewa wacce ta yamutsa kasuwar bayan fagen.

A cewar Shugaban Kungiyar ’Yan Canji na Jihar ta Adamawa, Lawan Mai Yasin, ’yan kasuwa sun tafka gagarumar asara a kwanaki bayan sun sayi Dalar a kan kusan N870, amma daga bisani ta karye zuwa N680.

Ya ce hakan ya jefa da yawa daga cikinsu a shakku, inda suka yanke shawarar jinkirtawa su ga yadda abubuwa za su koma don kaucewa sake tafka wata asarar.

“Yanzu ’yan kasuwa na da isassun kudade a kasa da suka saya da dan karen tsada, kafin farashin ya ci gaba da faduwa a cikin karshen makon nan. Saboda haka, yanzu akwai rashin tabbas a kasuwa, da yawa daga cikinmu ma yanzu sun daina sayen Dalar,” inji shi.

Su ma wasu masu sayen Dalar da Aminiya ta zanta da su sun koka cewa masu musayar kudin sun ki yarda su karbi canjin daga hannunsu.

A cewar wani kwastoma da ya ke aiki da wani kamfanin kasar waje da ya je don yin canjin, “Shagon canji daya ne ya yarda ya sayi Dala a hannuna ranar Asabar, saboda suna da ita da yawa a kasa, kuma suna tsoron tafka asara.

“Ko a ranar Lahadi ma da na sami mai saye, sai aka yi mun mugun tayi, inda na gwammace na mayar da ita gida har sai na ga abin da hali ya yi,” inji kwastoman.

A farkon makon nan ne dai farashin Dala ya yi tashi gwaurorn zabo, inda a wasu wuraren aka rika sayen kowacce a kan kusan N820.