✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana kokawar dibar mai daga fasasshen bututun mai

’Yan daba na kokawar dibar mai bayan bututun man kamfanin NNPC ya fashe.

Wasu gugun ’yan daba sun na rige-rigen dibar mai daga bututun man kamfanin NNPC da ke yoyo a Karamar Hukumar Amuwo-Odofin ta Jihar Legas.

Su ma masu sana’ar sayar da mai sun bi sahu wurin dibar man dizel din,  inda kowannensu ke ta kai-komo da jarkoki.

Mutanen sun yi watsi da kashedin da Hukumar Agajin ta Kasa (NEMA) ta yi cewa man da ke yoyi na iya yin bindiga, amma ko a jikinsu.

Jami’in NEMA mai kula da shiyyar Legas, Ibrahim Farinloya ta yi kira mazauna unuguwar Abule Osun da ke daura da Festac a Karamar Hukumar Amuwo Odofin cewa su kaurace wa yankin, don su tsira da rayuwarsu.

Ya bayyana cewa wuta na iya tashi daga man da ke tsiyaya yana bi ta yankin.