✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun kone gidan ’yan Shi’a a Kano

Sun ce an kone musu kaya na kusan miliyan uku a ciki

Wasu bata-garin matass sun kone ofishin Kungiyar ’Yan Uwa Musulmi (IMN) ta mabiya Shi’a da ke unguwar Dorayi Babba a Karamar Hukumar Gwale a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne sakamakon harin da suka kai wa gidan a kwanakin baya.

A wata hira da shugaban ofishin kingiyar Dokta Suleiman Gambo, ya yi da ’yan jarida a Kano, ya ce wasu bata gari ne suka tsallaka katangar ofishin, suka kuma cinna wa ginin wuta.

Ya ce a sakamakon haka, an kone musu kayan da suka kai na mlilyan uku.

Shugaban ya ce sun kai karar faruwar lamarin ga baturen ’yan sanda na Dorayi Babba, a inda ya je da kansa shi da wasu manyan jami’ansa, suka kuma gane wa idonsu irin barnar da aka yi musu.

Ofishin kungiyar wata matattara ce ga ’yan kungiyar, inda suke gudanar da taruka, da karatuttukansu na addini da kasuwanci da kuma adana kayayyaki na bukatu a unguwar.

A cewar shugaban, kafin faruwar wannan lamari, an kai wa wasu daga cikin ’ya’yan kungiyar ta su hari a ranar biyu ga watan Agusta yayin da suke gabatar da wani taro, inda aka ji wa wasu mutane biyar ciwo tare da kona wata motarsu.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kuma ce bai samu rahoton afkuwar lamarin ba, amma zai bincika da kuma daukar matakin da ya dace.