✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun tare hanya, sun kashe mutane a Jos

’Yan daba sun kona manyan motoci a tsakar daren.

Wasu ’yan daba sun tare babbar hanyar Gada-biyu da ke Jihar Filato a cikin dare inda suka kashe mutane tare da kona motoci.

Shaidu a garin Jos sun tabbatar mana cewa ’yan dabar sun kashe mutum biyu a lokacin da suka rika kai wa mutanen da ke wucewa farmaki.

’Yan dabar sun kuma rika cinna wa wasu manyan motoci da suka bi hanyar wuta a lamarin da ya faru kafin wayewar garin Laraba.

Ana zargin danyen aikin na da nasaba da rikicin Fulani makiyaya da mutanen Irigwe, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 20 baya ga daruruwan gidaje da aka kona a ranar Asabar.

Hakan kuma na faruwa ne bayan Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ba bayyana fushinsa kan rikicin na ranar Asabar, inda ya yi alkawarin tabbatar da an kamo an kuma hukunta duk masu hannu a ciki.

Bayan rikicin na ranar Asabar, an samu rahotanni da ke cewa an sake kona gidaje a kauyukan Jebbu da kuma Kpachu.