✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun tsarwatsa taron samar da tsaro a Arewa

An kai hari kan taron samar da tsaron da aka kira bayan harin Zabarmari

Wasu ’yan daba sun kai hari a zauren taron samar da tsaro a Arewacin Najeriya da ke gudana a Gidan Arewa House, Kaduna.

Fara taron ke da wuya, ’yan dauke da muggan makamai suka far wa zauren taron suka fatattaki mahalarta da masu jawabi tare da farfasa kayayyaki.

Mahalarta taron sun kunshi kwararru a fannin tsaro, sarakuna, shugabannin addini, kungiyoyi matasa, ’yan kasuwa da su.

Hotunan da aka yada bayan ’yan daba sun far wa zauren taron sun nuna yadda maharan suka farfasa kofofi da kujerun taron da aka shirya yinsa daga ranar Litinin zuwa Talata.

Zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto ba a kai ga samun cikakken bayani game da manufar maharan ba da kuma inda suka fito ba.

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ce ta kira taron na kwana biyu ne da zumman nema wa yankin da ma Najeriya mafita daga matsalar tsaro.

Kakakin Abdul-Azeez Suleiman ya sanar da taron ne bayan ya sanar da yanke kauna kan abin da ta kira katobarar da Gwamantin Tarayya ta yi bayan Boko Haram ta kashe manoma a Zabarmari, Jihar Borno.

CNG ta ce jazaman ne al’ummar Arewa su kare kansu, tunda Gwamnatin Buhari ta gaza, duk da rantsuwar da ya yi na kare rayukan ’yan Najeriya.

“Don haka CNG za ta gudanar da nabban taro kan tsaron Arewa daga 14 zuwa 15 ga Disamba, 2020 a Kaduna inda masana tsaro, sarakuna, malaman addini, kungiyoyi, ’yan kasuwa, matasa, mata da wakilan gwamnati za su tattauna.

“Taron zai lalubo hanyoyin samar da hadin kai a matakan jihohi da al’ummomi domin daukar matakan tsaro na bai-daya kuma a al’ummance tare da inganta hadin kai ta fuskar tsaro da samar da bayanai.

Ta yi kira da “a bincika a hukunta masu azurta kansu da kasuwanci a yaki da Boko Haram da kuma ikirarin nasarar da ake ta yi a yakin da duniya ke ganin koma baya a ciki.

“Muna Allahwadai da dukkanin nau’ikan manyan laifi da duk masu tunzurawa a aikata su a ko a karya doka a ko’ina a Najeriya”, inji ta.

CNG ta ce furucin jami’an gwamnatin bayan fushin da jama’a suka nuna kan kisan kiyashin da aka yi wa manoman shi ne makurar wauta da rashin damuwa da rayuwar al’umma.

“Tantagaryar shiririta, abin kyama, abin kunya da Allah-wadai ne irin kalaman da mashawartansa da ministocinsa suka yi game da mawuyacin halin da jama’ar Arewa ke ciki da ke bukatar daukar matakan gaggawa.

“Kashe-kashen na barazanar kawo yunwa tare da rusa kokarin samar da abinci musamman a Arewa inda masu satar mutane da ’yan bindiga ke hana manoma sakat”, inji CNG.

“Kisan Zabarmari ya yi fice ne saboda yawan mutanen da aka kashe a lokaci daya a kuma wuri guda, amma ya kamata duniya ta sani cewa ’yan ta’adda na yawan yin kisan kiyashi da satar mutanne musamman a Arewacin Najeriya”, inji sanarwar ta makon jiya.