✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun yi ta’adi a taron PDP a Gombe

Na yi imanin cewa an kai harin ne saboda na bar APC zuwa PDP.

Akalla mutane biyar ne suka jikkata a wani hari da ’yan daba suka kai wa taron PDP da aka gudanar a Unguwar Jekadafari a Jihar Gombe.

Aminiya ta ruwaito cewa, PDP ta gudanar da taron ne a gidan wani jigonta, Alhaji Salihu Abdulaziz wanda aka fi Sani da Salisu Mista B.

An gudanar da taron ne bayan da Salisu Mista B, wanda mamba ne a jam’iyyar APC mai mulki ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Mista B ya shirya taron ne saboda mata da matasa domin karbar bakoncin dan takarar Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa wanda kuma shi ne tsohon gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo.

Bayanai sun ce ana tsakar taron ne ’yan daba wadanda aka fi sani da ’yan kalare a Gombe da kewaye suka mamaye gidan dauke da makamai daban-daban.

A cewar Mista B yayin zantawarsa da manema labarai, ’yan kalaren sun kai harin ne kan mai uwa da wabi a kan wadanda suka halarci taron.

Ya ce ’yan kalaren sun yi masa barna ciki har da karya masa kyaure da dukkan fitulun wutar lantarki da tagogin gidansa.

Sai dai ya ce an yi sa’a ’yan sanda sun kawo dauki da gaggawar, lamarin ke nan da ya kwantar da tarzomar.

Ya kara da cewa yana zargin harin ya faru ne a sakamakon ficewar da ya yi daga jam’iyyar APC.

Mista B ya ce yanke shawarar raba gari da jam’iyyar PDP wanda ya ce ta gaza ceto jihar daga kalubale daban-daban da suka hada da talauci da kuncin rayuwa.

“Na yi imanin cewa an kai harin ne saboda na bar APC zuwa PDP,” inji shi.

Aminiya ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, inda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce akalla mutane biyar ne suka samu rauni, kuma ‘yan sanda sun mika su zuwa asibiti.

Sai dai ASP Mahid ya ce har yanzu ba su kai ga samun nasarar kama kowa kan wannan harin ba, amma suna ci gaba da gudanar da bincike.