✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan dagajin siyasa ne ke canja sheka

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya ce ’yan siyasar da suke barin jam’iyyunsu na asali suna canja sheka zuwa wasu jam’iyyu, ’yan…

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya ce ’yan siyasar da suke barin jam’iyyunsu na asali suna canja sheka zuwa wasu jam’iyyu, ’yan dagajin siyasa ne da suka shiga siyasa don biyan bukatar kansu ba don talakawa ba.

Sanata Bukar Abba ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai, inda ya ce ’yan siyasa da zababbun ’yan siyasar da ke canja sheka zuwa wata jam’iyyar da ba ita ta kai su kan matsayin da suke kai ba, suna yi ne don tsananin zarmiya da rashin sanin ya kamata.

Tsohon Sanatan wanda ya wakilci Gabashin Jihar Yobe a Majalisar Dattawa, ya yi tir da yadda wadansu ke barin jam’iyyar da suka biyo ta kanta don zama matsayin da suke kai zuwa wata jam’iyyar da suke hangen ta fi tasu.

Ya nemi hukumomi da jam’iyyu su samar da wata kwakkwarar doka da za ta haramta irin wannan lamari na rashin akida, ganin cewa hakan kan haifar da rudani a harkokin siyasa. Ya ce hakan zai magance tsalletsallen da ’yan siyasa musamman masu rike da madafun iko ke yi tare da karfafa harkokin dimokuradiyya.

Ya ce, “Irin wannan halayya ta yawaitar canja sheka ba ana yi ne ba tare da dalilai ba, to amma a ganina hakan ba zai zama alheri ga kasa.”

Kuma a matsayinmu na ’yan Adam dole ne lokaci zuwa lokaci a rika samun rashin fahimta a tsakanin al’umma, to amma duk da haka a tsaya a sasanta a tafi tare a cire son zuciya,” inji shi.

Da ake tambaye shi kan yiwuwar wata rana ya canja sheka zuwa wata jam’iyyar da ba APC ba? Sai jagoran na APC ya ce, “Ai ni mai akida ne da ra’ayi daya, don haka ba zan taba barin akidata ta kaifi daya da nake kai a tsawon rayuwata ba.”

Tsohon Gwamnan ya yaba wa Majalisar Dokoki ta Kasa kan ayyukanta, kuma ya kalubalanci mutanen da ke zargin ’yan majalisar da cewa ’yan amshin shata ne, wai suna bin bangaren gwamnati sau-da-kafa maimakon turjiya da cewa hakan aikin kawai ne.

Ya kara da cewa majalisar a yanzu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da dokokin da al’ummar kasa za su amfana, kuma babu wata kasa a duniya da za ta wanzu ba tare da dokoki ba. “Don haka, ban amince da cewa majalisar ’yar amshin shata ba ce ga Bangaren Zartarwa,” inji shi.

Kuma ya ce zai sake tsayawa takarar kujerar Majalisar Dattawa a zaben badi don komawa majalisar da nufin ci gaba da ba da gudunmawarsa ga yankinsa da jiharsa da kasa baki daya na shekara 4 sannan ya yi murabus.

Ya ce, “Na shafe kusan shekara 12 a Majalisar Dattawa, na kuma bar majalisar kusan shekara uku na ga abubuwa masu yawa musamman kan abin da ya shafi tabarbarewar tsaro da ke bukatar a yi gyare-gyare a kai a kasa baki daya, duk da cewa majalisar ba ta da ikon gudanar da komai dole sai da hadin gwiwar Majalisar Wakilai da kuma Majalisar Zartarwa.