✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan damfarar intanet 4 sun mutu bayan sun yi mankas da kwayoyi a Bayelsa

Daya daga cikinsu da bai rasu ba ne ya tabbatar da haka ga 'yan sanda

Wasu ’yan damfarar intanet da aka fi sani da ‘Yahoo boys’ su hudu sun mutu bayan sun yi mankas da miyagun kwayoyi a Jihar Bayelsa.

’Yan sanda sun ce lamarin ya auku ne a yankin Biogbolo da ke Yenagoa, babban birnin jihar.

’Yan sandan sun kuma ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 12:00 na daren Juma’a, lokacin da suke tsaka da sharholiya bayan wani babban kulli da suka taka.

Wani mai suna Melvin, wanda ya bayyana kansa a matsayin abokin daya daga cikin wadanda suka mutun ya ce sun gamu da ajalin nasu ne a cikin wani gida da daga cikinsu mai suna Favour ta karbi hayarsa.

Melvin ya kuma shaida wa ’yan jarida cewa yanzu haka suna kokarin karbo gawar Favour mai shekara 19.

Ya ce, “Muna tunanin guba aka saka musu. Yanzu haka muna ofishin ’yan sanda na Ekeki tare da mahaifin Favour domin karbar gawarta mu je mu birne ta.

“Mun fahimci cewa sun mutu ne bayan cin wani abinci mai dauke da guba, wanda wani dan aiki ya kai musu. Amma daya daga cikinsu wanda ya zagaya bandaki bai ci abincin ba, bai mutu ba,” inji Melvin.

Shi ma wani abokin mamatan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Lokacin da muka tilasta wa mai gadin gidan balle kofa don mu shiga, ba su mutu ba. Nelson (daya daga cikinsu) na zaune a kan kujera amma kansa na kasa ya yi amai.

“Bisa ga dukkan alamu dai guba suka ci,” inji shi.

Sai dai Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Benjamin Okolo, wanda ya tabbatar da rasuwar matasan su hudu, ya ce sun mutu ne sanadin shan kwayoyi.

Ya ce, “Sun mutu ne bayan sun yi mankas da kwayoyi. Hakan abin takaici. Su biyar ne, amma mutum daya bai mutu ba, shi ya fada mana cewa kowa daga cikinsu ya sha kwayar guda biyu. Abin da ya kashe su ke nan,” inji Kwamishinan ’Yan Sandan.