✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan fada sun kange Buhari daga masu fadar gaskiya —Dalung

Suna fakewa da COVID-19 su hana masu fada masa gaskiya ganin shi.

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung ya koka kan abin da ya kira wadansu makusantan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suna kange shi daga masu kokarin dora shi a turba tagari da yi wa ’yan kasa hidima.

Solomon Dalung ya ce na kusa da Shugaban Kasar sukan ba da uzuri na bogi cewa akwai annobar COVID-19 don haka ba za a iya ganawa da shi ba.

  1. SAURARI: Yadda ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano
  2. Bankin Duniya Na Bin Ko Wanne Dan Najeriya N24,000
  3. Gwamnoni sun fi Gwamnatin Tarayya barna – Baba-Ahmed

Ya bayyana haka ne yayin hira da kafar labarai ta Legit a ranar Litinin da ta gabata.

Da aka tambaye shi game da aikin da na kusa da Shugaban suke yi don ganin sun wanke Najeriya daga kunya a idon duniya, musamman a fannin tsaro, Mista Dalung ya ce, “Yana yiwuwa wadanda suke kange Shugaban Kasa yanzu ba sa son a ba shi wata shawara a kan abin da yake faruwa.

“Ke nan suna da niyyar su ba shi kunya da rushe kyakkyawar manufar da yake da ita, shi ya sa suka hanawa tare da kange mutane zuwa jikinsa.

“Ai yana zuwa taro, yana karbar baki, muna ganin yana karbar mutane, wadannan mutanen ba su da COVID-19 ne? Ko sai mu da za mu zo mu gan shi ne za mu cutar da shi?”

Game da zargin Shugaba Buhari da gazawa wajen magance matsalar tsaro, Mista Dalung ya ce Shugaban bai gaza ba.

“Ina ganin kamar matsalar tsaro da aka shiga, wadda ’yan Najeriya suke fama da ita a kowace rana, da zargin Shugaban Kasa cewa ya gaza, ina ganin ba lallai ya gaza ba ne.

“Amma wane irin bayani yake zuwa gare shi? Shin abubuwan da suke faruwa yana jin su kamar yadda suke faruwa?

“A nawa tunanin Shugaban Kasa ya shiga halin da mutane wadanda za su ba shi shawara mai kyau sai dai su je kusa da shi su kadai.

“Wannan a yi addu’a ga Allah, Allah Ya taimaki Shugaban Kasa ya fita daga cikin wannan hali,” inji shi.