✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fansho na barazanar rufe filayen jirgin sama

’Yan fanshon Hukumar Filayen Jiragen Saman na barazanar rufe su saboda nuna musu bambanci

Tsoffin ma’aikatan Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman ta Najeriya (FAAN) na barazanar rufe tashoshin jiragen saman saboda bambancin da ake nunawa wajen biyan su.

’Yan fanshon sun ba wa FAAN wa’adin ranar 4 ga watan Mayu, 2021, su magance matsalar, idan kuma suka ki, to za su fuskanci bore a fadin Najeriya.

Sun bayar da wa’adin ne a yayin wani gangami da Kungiyar ’Yan Fansho ta Kasa (NUP) ta gudanar a Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed (MMA) da ke Legas.

A ganawarsa da ’yan jarida, Sakataren Kasa na NUP, reshen FAAN, Kwamared Emeka Njoku ya zargi hukumar gudanarwar FAAN ta yi biris da dokar ka’idojin aiki da aka amince da yi a zaman da aka yi kan bambancin kudaden.