✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fansho sun tarwatsa bikin rantsar da sabbin Ciyamomi a Neja

Suna zanga-zanga ne kan kin biyansu hakkokinsu na tsawon shekara bakwai

’Yan fansho a jihar Neja sun tarwatsa bikin rantsar da sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi su 25 da aka yi a jihar saboda kin biyan su kudaden da suke bi bashi.

’Yan fanshon dai sun zargi gwamnatin jihar da kin biyan su kudaden fansho da na garatutin da suke bi har na tsawon shekara bakwai.

Rahotanni sun ce wannan kusan ita ce zanga-zanga irinta ta uku a jere da mutanen ke gudanarwa a Gidan Gwamnatin Jihar.

Lokacin da ’yan fansho suka tarwatsa taron Neja
Lokacin da ’yan fansho suka tarwatsa taron Neja

Jaridar The Nation ta rawaito cewa ’yan fanshon sun kulle kofar shiga gidan gwamnatin, inda suka hana bakin da suka je rantsar da Ciyamomin shiga.

Sun dai zargi gwamnatin da nuna halin ko-in-kula da halin da suke ciki na tsawon shekara bakwai, duk da abin da suka kira yaudararsu da aka yi ta yi ta hanyar tantance su.

Daya daga cikinsu, mai suna Abubakar Abdullahi ya bayyana Gwamnatin Jihar a matsayin maketaciya.

“Ta yaya zaka hana mutum hakkinsa tsawon wannan lokacin kuma ka yi mursisi kamar babu abin da ya faru?,” inji Abubakar.

Ita ma wata ’yar fanshon mai suna Charity Yusuf, ta ce gwamnatin ta gaza ciki duk alkawuran da ta yi musu a baya, duk kuwa da cewa ta karbi makudan kudade daga Gwamnatin Tarayya.