✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fashin banki sun kashe jama’a, sun debi makamai a Kogi

Wasu gugun ‘yan fashi sun hallaka mutane da dama a wani hari da suka kai da tsakar rana a wani banki da ke jihar Kogi.…

Wasu gugun ‘yan fashi sun hallaka mutane da dama a wani hari da suka kai da tsakar rana a wani banki da ke jihar Kogi.

Harin na yankin Isanlu a karamar hukumar Yagba ta Gabas ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama, ciki har da na jami’an tsaro da ma’akatan banki da kwastomomin reshen na First Bank.

Hakazalika ‘yan fashin sun kai farmaki a babban ofishin ‘yan sandan yankin inda a nan ma suka kashe ‘yan sandan da ke wurin.

Yayin hada wannan rahoto Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi DSP William Ayah ya ce ya gaza ganawa ta waya da DPO ko wasu jami’an ‘yan sandan yankin da aka kai wa harin domin ba su amsa kiran waya ba.

Ya ce mai taimaka wa kwamishinan ‘yan sandan jihar a fannin ayyuka ya isa wurin yana kuma tattara bayanai.

“Jama’ar yan kin sun kawo rahoton harin ‘yan fashin a bankin da ofishin ‘yan sanda, amma ni ba zan iya baku cikakken bayanai ba, domin mun gaza samun DPO na yankin ta wayar salula.

Amma Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da ayyuka na wajen domin bibiyar lamarin da ya faru” inji DSP Ayah.

Yace, “Wata majiya ta ce sun kai hari a ofishin ‘yan sandan tare da hallaka daukacin jami’ain da suka gani.

“Sun yi barna sossai sun kuma arce da makamai. Su kusan 7 ne suka durfafi bankin  ne a motoci biyu, inda suka hallaka mutane da dama.

“Sai da suka kashe jami’an da ke ba da tsaro a bankin kafin su samu shiga cikin bankin inda suka hallaka wasu ma’aikatan bankin da wasu kwastomomi.

“Yan fashin sun kwashe fiye da awa guda kafin su arce a cikin motocinsu,” inji kakakin ‘yan sandan kamar yadda ya shaida wa wakilinmu ta wayar salula.

Wasu da suka shaida faruwar lamarin sun ce fashin bankin ya yi kama da irin wanda ya faru a baya a garin Offa na jihar Kwara.

Wani bangare na bankin da ‘yan fashin suka fasa.