✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fim ba Malamai ba ne – Zainab Booth

Hajiya Zainab Booth daya daga cikin manyan jaruman fina-finan Hausa ta mayar wa Mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara a kan harkar addinai, Ali Baba…

Hajiya Zainab Booth daya daga cikin manyan jaruman fina-finan Hausa ta mayar wa Mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara a kan harkar addinai, Ali Baba Fagge, wanda ake yi wa lakabi da ‘A Gama Lafiya’ martani dangane da wasu kalamai da ya yi, a inda ya kira masu shirin fim malamai, ya kuma kwatanta irin ayyukan da suke yi wa al’umma tamkar na Hisba idan ma ba su fi su ba.
Ali Baba wanda ya yi wadannan kalamai a wata hira da ya yi da wakilin wani gidan rediyo mai zaman kansa a a Jihar Kano, ya nuna cewa masu shirin fina-finai su ma malamai ne da suke aikin Allah ta hanyar umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna.
Kalaman sun haifar da cece-kuce domin a bayanin nasa bai ware raye-raye da wake-waken da ‘yan fim din suke yi ba wadanda  mutane suke yi wa Allah wadai saboda ganin cewa sun kauce wa addini da kuma ala’ada, amma sai ya ce wannan ba laifi ba ne.
 Hajiya Zainab Booth ta ce akwai kuskure a kalaman da Ali Baba ya yi. ‘Yan fim ba malamai ba ne, ba kuma ba za su taba hada kafada da magada annabawa ba.
Ta mayar da wannan martani ne a gidan rediyon da Ali Baban ya ya yi wadancan kalamai.
Zainab Booth, ba ya ga fitowa da take yi a fina-finai, ta aurar da ‘yarta ga jarumi Yakubu Muhammad, sannan ‘yarta Maryam Booth da kanenta Amude duk zuna fitowa a fina finan Hausa,
Ba wannan ne karo na farko da Ali Baba ya taba yin irin wannan furuci ba. A baya ya ce jahilai ne kadai ba su fahimci inda masu shirin fim suka sa gaba ba.