✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fim da mawaka kusan 100 za su halarci shagalin Sallah na Rarara a Kano

Za a shafe tsawon mako guda dai ana rakashewa yayin bikin

Akalla jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood 100 ne za su halarci shagalin Sallah da fitaccen mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara ya shirya a Kano.

Kungiyar mawakan nan da ake wa lakabi da 13×13, wacce ke karkashin mawakin ta ce za a kwashe tsawon mako daya ana rakashewa tare da nishadantar da masoya wakokin Hausa.

Bikin, wanda shi ne irin shi na farko dai an yi masa lakabi da ‘Arewa Sallah Festival’, kuma zai kasance karkashin Rararan.

Rahotanni sun ce za a fara bikin ne tun karfe 3:30 na yamma har zuwa 7:00 na yamma a kullum.

Za a gudanar da bikin ne a gidan adana namun daji na Kano (Zoo), sabanin dandalin kasuwar duniya da ke Kano.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa jarumai da mawaka kimanin 100 ne za su gwangwaje a bikin.

Daga cikin wadanda za su halarci bikin akwai Rarara da Aminu Ladan (Ala) da Yakubu Mohammed da Adam A. Zango da Umar M. Shareef da Nura M. Inuwa da Ali Jita da Baban Chinedu da El-Mu’az Birniwa da Auta MG Boy da Abdul D. One da dai sauransu.