✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan gudun hijira miliyan 2 ne yanzu a Najeriya – Minista

Ministar ta ce rikicin Boko Haram, ta'addanci, Garkuwa da mutane ne ya yi sanadin haifar da 'yan gudun hijirar.

Ministar Jinkai, Agajin Gaggawa da Walwalar Jama’a ta kasa, Sadiya Umar-Farouk ta ce yanzu haka Najeriya na da ‘yan gudun hijira miliyan biyu.

Ministar ta bayyana hakan ne yayin da take amsa tambayoyin ‘yan jarida a Abuja ranar Alhamis game da ‘yan gudun hijira.

Sadiya ta ce, “Yanzu a Najeriya muna da ‘yan gudun hijira akalla miliyan biyu, wadanda matsalar ta’addanci ta ritsa da su.

“Aikin ma’aikatar nan shi ne samar da tallafi, da hanyoyin kyautata rayuwar wanda rikicin ta’addanci ya shafe su.

“Ma’aikatar nan na kokarin ganin an tallafi ‘yan gudun hijirar, wajen dawo da su muhalallansu, wasu kuma a gina musu gidajensu da suka rasa,” inji ministar.

Sadiya, ta kuma kara da cewa APC ita ce jam’iyya ta farko da ta taimaki masu bukata ta musamman, tun daga matakin mazabu har zuwa matakin tarayya.

A cewar Sadiya, shugaba Buhari na da shirin bada mukami daga cikin masu bukata ta musamman a cikin gwamnatinsa.

Idan ba a manta ba, a baya shugaban ya nada mai ba shi shawara na musamman a kan masu bukata ta musamman.