✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai wa ’yan majalisa hari

’Yan Majalisar sun sha da kyar a hanyar su ta dawowa daga jana’iza.

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa uku sun tsallake rijiya da baya a hannun ’yan ina-da-kisa da suka kusa aika su lahira.

’Yan majalisar sun yi gamo da ’yan ina-da-kisa ne a lokacin da suke hanyarsu ta komawa garin Lafia, bayan sun halarci jana’iza a Karamar Hukumar Akwanga ta Jihar.

Mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Jibrin Gwamna, ya ce, “’Yan majalisar na hanyarsu ta dawowa daga jana’izar matar dan uwan Honorabul Tsebe ne lokacin da ’yan ina-da-kisa suka bude wa motar Honorabul Tsebe wuta a kauyen Wowyen da ke hanyar Akwanga zuwa Lafia.”

Da misalin karfe 10 na safiyar Laraba ne ’yan ina-da-kisa suka yi wa Honorabul David Maiyaki da Peter Akwe da Samuel Tsebe, kwanto a hanyarsu ta dawowa daga jana’izar matar wan Honorabul Tsebe da ta rasu.

Ana zargin Honorabul Samuel Tsebe ne ’yan ina-da-kisan suka so hallakawa, saboda motocin ’yan majalisar su uku sun yi jerin gwano, amma tasa ce a karshe kuma ita aka bude wa wuta.

Yadda muka tsallake rijiya da baya —Dan majalisa

Honorabul Tsebe, wanda ya tsallake rijiya da baya, ya tabbatar wa wakilinmu abin da ya faru, sannan ya yi godiya ga Allah da Ya kubutar da shi da takwarorin nasa.

“Mun nufo kauyen Wowyen da ke kan hanyar Akwanga zuwa Lafia,  tsakanin Kwalejin ’Yan Sandan Kwantar da Tarzoma da Dutsen Ende Hills da kauyen ta bangaren gada.

“Kawai sai na ji karar harbi ta bangaren direba a motata kuma ni nake tuki a lokacin.

“Harsasihin ya fasa gilasan motar wadda direbanta aka so a harbe, kuma a lokacin ni ke tuki, shi ya sa muke zargin ni aka nufa da harin.

“Bisa dukkan alamu wanda ya yi yana lura da duk motsina kuma ya san nine nake tuka motar a lokacin.

“Yunkurin ’yan ina-da-kisa ne kuma na sanar ’yan sanda abin da ya faru.

“Muna godiya ga Allah da Ya tseratar da mu,” inji dan majalisar.