✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan IPOB na neman kawo cikas a kotun da ake shari’ar Kanu

Sai dai da adadinsu ya ci gaba da karuwa, ’yan sanda sun tarwatsa su.

’Yan sanda a ranar Litinin sun tarwatsa wasu ’yan haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB wadanda suka yi wa Babbar Kotun Tarayyar da ke yi wa jagoransu, Nnamdi Kanu shari’a kawanya.

Fusatattun mambobin kungiyar dai sun mamaye kotun da ke zamanta a Abuja ne gabanin fara shari’ar tasa ranar Litinin.

Daya daga cikin matasan sanye da bakaken kaya ya yi wa ’yan jarida jawabi amma da harshen Ibo.

Sai dai yayin da adadin masu tarzomar ya ci gaba da karuwa, sai ’yan sanda suka tarwatsa su.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a riga an kawo Nnamdi Kanu kotun ba.

An hana wasu ’yan jarida shiga kotun

Rahotanni sun ce kafafen yada labarai 10 ne kawai jami’an tsaro suka sahale wa shiga domin kallon shari’ar, duk kuwa da cewa bai kamata a hana su shigar ba.

Yadda ’yan jaridar da aka hana shiga suka yi curko-curko a harabar kotun.

Wata takarda da wakilin Aminiya ya gani daga kotun ta nuna sunan ’yan jarida 10 ne kawai, sai masu daukar hoto mutum hudu aka bari su shiga kotun.

Jerin kafafen yada labarai guda 10 da aka amincewa shiga kotun.

Wakilin namu wanda ya halarci kotun tun misalin karfe 6:45 na safiyar Litinin ya fuskanci cikas daga jami’an tsaro wadanda suka umarce shi ya juya saboda sunansa ba ya cikin wannnan takardar.

“Ko da na karasa kotun, sai jami’an tsaro suka umarceni da in koma saboda babu sunana a cikin jerin wadanda aka amince wa su dauki rahoton shari’ar,” inji wakilin namu.

“Yanzu haka ma ga mu nan a waje mun yi cirko-cirko, muna jiran abin da ka je ya zo.”

Kanu, wanda tun bayan kamun da aka yi masa tare da dawo da shi Najeriya yake hannun DSS, ya roki kotun da ta mayar da shi Gidan Yarin Kuje a daga hannun DSS din.

Bayan dawo da shi Najeriya, Mai Shari’a Binta Murtala Nyako wacce a baya ta bayar da shi beli bisa dalilai na rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun DSS har zuwa 26 ga watan Yuli, 2021.