✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan IPOB sun fille kan sojoji mata da miji a Imo

Sun kuma kira iyalan sojojin suna barazanar su ma za su kashe su

’Yan kungiyar awaren Biyafara na IPOB a Jihar Imo sun harbe wasu sojoji mata da miji sannan suka fille musu kai suka dora a kan gawarwakinsu.

Wata majiyar hukumar tsaro ta bayyana wa jaridar Sahara Reporters cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar ga wani soja mai suna A.M Linus mai mukamin Sajent da kuma matarsa mai mukamin Kofar.

Rahotanni sun ce an kashe su ne lokacin da suke hanyarsu ta zuwa Jihar ta Imo.

A cewar jaridar, ’yan awaren sun kuma fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda suka raba gangar jikin sojojin da jikinsu tare da dora kawunansu akan kirjinsu inda daga bisani suka kira iyalan mamatan domin shaida musu lamarin.

Wani soja ya shaida wa Sahara Reporters cewa, “Ranar Asabar abin ya faru suna kan hanyarsu ne ta zuwa Imo. Bayan sun yi wannan aika-aikar sai kuma suka yi amfani da wayoyinsu domin kiran ’yan uwansu su shaida musu kisan, tare da yi wa musu barazanar kashe su su ma.

“Wadannan ma’auratan gabanin aurensu mutane da dama sun soki auren nasu saboda shi sojan kafin ya auri matar an ce yana da mata har da ’ya’ya, haka ita ma an ce tana da yara gabanin ta shiga aikin soja,” inji majiyar.

A baya-bayan nan dai hare-hare a kan jami’an tsaro na kara karuwa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ana danganta wannan hari da kungiyar nan ta IPOB, sai dai kungiyar ta musunta zargin da ake mata.

A halin yanzu dai Shugaban kungiyar, Nnamdi Kanu, na tsare a Abuja inda yake fuskantar shari’a kan zarginsa da ake yi da cin amanar kasa.