✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan IPOB sun kashe Shugaban Hukumar Shige da Fice a Imo

Kisan gillar guda ce cikin manyan mutanen da aka kashe cikin kwana uku a Jihar. 

Wadansu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan awaren IPOB ne sun harbe babban jami’in hukumar shige da fice ta Najeriya mai kula da Jihar Imo, Okiemute Mrere.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kashe jami’in ne tun ranar Asabar da daddare a kan babbar hanyar Owerri zuwa Fatakwal, inda aka gano gawarsa yashe cikin wani jeji da safiyar Lahadi. 

Bayanai sun nuna cewa an kashe jami’in ne yayin da yake tuka motar a-kori-kura ta Hukumar inda maharan suka cimma sa kuma suka harbe shi. 

Sai dai babu abin da ‘yan bindigar suka dauka a cikin motar, ciki har da karamar bindigarsa wacce aka tarar da ita kan gawarsa washe gari.  

Wakilinmu ya ruwaito cewa, motar hukumar da aka kashe shi a cikinta, ruwan harsasai ya yi mata mummunar illa. 

Kakakin Hukumar a jihar, Winifred Oguh, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce har yanzu hukumar ba ta samu cikakken bayani dangane da kisan gillar Shugaban nata ba, sai dai suna ci gaba da binciken lamarin. 

“Ina mai tabbatar da cewa mun rasa guda cikin jami’anmu, DSI Mrere. 

“Bamu samu cikakken bayani ba tukunna saboda har yanzu muna ci gaba da gudanar da binciken kan lamarin,” a cewar Winifred. 

Kisan gillar jami’in, guda ne cikin manyan mutanen da aka kashe cikin kwana uku a jihar. 

A ranar Asabar din ce aka kashe hadimin tsohon Shugaban Kasa kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, yayin da yake kan hanyar zuwa tashar jiragen saman Sam Mbakwe da ke Jihar domin komawa Abuja.