‘Yan jagaliya sun yi wa Majalisar Dokokin Jihar Ondo zobe | Aminiya

‘Yan jagaliya sun yi wa Majalisar Dokokin Jihar Ondo zobe

    Ishaq Isma'il

Wasu mutane da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun mamaye Majalisar Dokokin Jihar Ondo da safiyar Litinin kamar yadda rahotanni suka bayyana.

’Yan bangar sun yi wa farfajiyar majalisar kutse na bazata a yayin da ake tsammanin dawowar wasu ’yan Majalisar hudu magoya bayan Agboola Ajayi, Mataimakin Gwamnan Jihar.

’Yan Majalisar da ake tsammanin isowarsu sun hadar da; Ogundeji Iroju; Wale Williams; Tomide Akinribido da Favour Tomomowo.

Uku daga cikinsu ’yan jam’iyyar ne sai kuma Akinribido dan jam’iyyar ZLP, wadda Mataimakin Gwamnan ya sauya sheka zuwa cikinta bayan ya rasa tikitin takara na zaben Gwamnan Jihar a Jam’iyyar PDP.

A baya-bayan nan ne wata babbar kotu ta soke hukuncin da Majalisar Dokokin ta aiwatar na dakatar da ’yan majalisar hudu daga halartar zamanta da sauran harkoki.

A halin yanzu dai Mataimakin Gwamnan shi ne dan takatar gwamnan jam’iyyar ZLP wanda zai fafata a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba.