✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan jarida sun kaurace wa ayyukan gwamnatin Yobe

Kungiyar Wakilan Kafofin Yada Labarai (Correspondents Chapel) da ke karkashin Kungiyar ’Yan Jarida ta kasa reshen jihar Yobe (NUJ) reshen Jihar Yobe ta kauracewa duk…

Kungiyar Wakilan Kafofin Yada Labarai (Correspondents Chapel) da ke karkashin Kungiyar ’Yan Jarida ta kasa reshen jihar Yobe (NUJ) reshen Jihar Yobe ta kauracewa duk wasu ayyukan gwamnatin jihar saboda tursasawa da cin zarafin da jami’an tsaron da ke gidan gwamnatin jihar  ke yi wa mambobinta da wasu dalilai.

Matakin kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaba da  kuma sakataren kungiyar Mista Ahmed Abba da Mista Michael Oshomah suka sanya wa hannu ranar Juma’a a Damaturu.

Abubuwan da ke kunshe cikin wannan sanarwar sune kamar haka:

Kungiyar NUJ reshen Jihar Yobe, a taronta na gaggawa da ta gudanar a ranar Juma’a, 28 ga watan Oktoba, 2022, ta yanke shawarar kaurace wa dukkan ayyukan gwamnatin jihar saboda dalilai kamar haka:

1. Cin zarafi da jami’an tsaro ke yi wa mambobin ta a gidan gwamnati.

2. Rashin gayyata a hukumance zuwa ayyukan gwamnati.  A matsayinmu na bangare  na hudu wabda aikinmu shi ne sanar da jama’a abubuwan da ke faruwa a jihar ciki har da gidan gwamnati.

Sai dai kuma abin takaicin shi ne sama da shekara guda da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta yi, mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, bai taba aika goron gayyata a hukumance ba domin a kawo rahotannin ayyukan gwamnan ga kungiyar ba sabanin yadda aka saba a baya.

Hakan na kawo nakasu ga ayyukan wakilan kungiyar jaridun na kasa da ke aiki a jihar.

3. Rashin samun damar saduwa da  Gwamna Mai Mala Buni ta hanyar ’yan jarida masu aiki a jihar.

Don haka ne kungiyar wakilan kafofin yada labaran ta ga cewa abin ya dami mambobinta duk da cewa gwamnan ya yi tarihi a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa.

Kuma ya yi gwamna sama da shekaru 3 inda yake jawabi ga manema labarai a Abuja da sauran sassan kasar nan, amma bai taba yin jawabi ga wakilan jaridun kasa da ke jihar ba musamman don yin magana kan manufofin gwamnatinsa da shirye-shiryensa, wanda hakan ke tabbatar da rashin isarsa ga ’yan jarida mazauna jihar.

4. Kungiyar ta yanke shawarar cewa mambobinta za su daina amfani da duk wata sanarwar ko labarin da gwamnatin jihar Yobe ta fitar ba tare da tuntubar bangaren shugabancin kungiyar  ba.

Don haka kungiyar ta yi kira ga shugabannin hukumomin tsaro a jihar da su wayar da kan jami’ansu kan harkokin tsaro a kafafen yada labarai.

Ya zama dole kungiyar ta dauki wannan matsaya mai mahimmanci domin fadakar da masu ruwa da tsaki da hukumomin da suka dace don daukar kwararan matakai don magance matsalolin da ke akwai kan wannan lamari cikin ruwan sanyi.

Daga karshe kungiyar wakilan kafofin yada da ke aiki a jihar Yobe suna son sanar da jama’a da gwamnatin jihar Yobe cewa matakin da muka dauka bai kamata a yi hukunci da son rai ba, a’a, a matsayinmu na daya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin dimokuradiyyarmu, akwai bukatar da a yi mana duba na adalci dangane da wannan lamari.

Haka nan yana da mahimmanci a lura cewa zaɓe mai zuwa yana da matukar muhimmanci a dimokuradiyyar ƙasarmu don haka kuskure ne a yi watsi da ’yan jarida mazauna Jihar kan duk wasu harkokin da suka shafi siyasa a jihar.