✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan jarida za su karrama fitattun ’yan Najeriya 7 a Kano

Wakilan Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa reshen jihar Kano, ta shirya wani babban taro domin karrama wasu fitattun ’yan Najeriya bisa la’akari da gudunmuwar da…

Wakilan Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa reshen jihar Kano, ta shirya wani babban taro domin karrama wasu fitattun ’yan Najeriya bisa la’akari da gudunmuwar da suka bayar ga ci gaban kasa da kuma amincewarsu da kafafen yada labarai na Najeriya.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Wakilan, Mustapha Hodi Adamu, ta nuna cewa za a gudanar da gagarumin taron ne a ranar 28 ga watan Nuwamba a Otel din Bristol Palace da ke Farm Centre a birnin Kano.

Daga cikin wadanda za a karrama akwai Lauyan Koli kuma Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami (SAN); Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwar Zamani (NITDA), Malam Kashifu Inuwa.

Sauran sun hada da Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Kano, Habu Sani; Kwamishinan Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba; da Shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa, Muhuyi Magaji Rimingado.

Akwai kuma Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya, Kabiru Alhassan Rurum da Shugaban Kamfanin Shinkafa na Umza Rice Limited, Alhaji Muhammad Abubakar Mai fata.

Sanarwar ta kara da cewa wadanda za a karrama sun kasance mazan kwarai wadanda aka tabbatar da gaskiyarsu gami da adalci a yayin da suka yi fice a fannoni daban-daban na gwagwarmayar rayuwa.