✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan kabilar Ibo ke ganin tasku saboda sun musulunta

Tsangwamar da ake wa Musulmai ’yan kabilar Ibo ta sa su hijira daga garuruwansu.

Musulmai ’yan kabilar Ibo na kaura daga Kudu Maso Gabas zuwa Arewacin Najeriya, sakamakon tashin hankalin da ake samu a yankin, kamar yadda wani binciken Aminiya ya gano.

Matsalar tsaron da masu karajin kafa kasar Biyafara (IPOB) ke haddasawa yankin ta jefa rayuwar Musulmai ’yan kabilar Ibo cikin matsanancin hali.

Binciken ya gano cewar Musulmai Ibo a jihohin Abiya, da Anambra, da Ebonyi, da Enugu da Imo suna kaura zuwa Arewa don samun mafaka tare da yin ibada yadda ba tare da tsangwama ba.

Wasu daga cikinsu da sun bayyana mana irin bakar wahala, wariya da kuma tsangwama da suke fuskanta a yankin na Kudu maso Gabas.

‘Ba mu da ’yanci’

A tattaunawar da aka yi da shi, Mataimakin Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Sheikh Haroun Ajah, ya bayyana irin cikas da Musulman ke samu a yankin.

“Musulmai ba su da damar yin addininsu, ba a nada mu a wasu mukaman siyasa, sannan ba mu da damar shiga wata sabga ta gwamnati — da suna da damar hana mu cin abinci da sun yi.

“Idan suka ga Ibo Musulmi suna daukar shi Bahaushe ne, sun kasa gane cewar Hausa da Ibo kabilu ne, shi kuma Musulunci wata hanya ce ta bauta wa Mahalicci”, inji Shaikh Haroun.

Ya kuma ce adadin Musulman Ibo da ke Arewa ya zarta na daukacin  yankin Kudu-maso-Gabas.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta shiga lamarin don kawo karshen wariya da ake nuna wa Ibo Musulmai.

Shi ma a bangarensa, Babban Limamin Jihar Imo, Suleiman Njoku, ya bayyana cewa, “Da yawa daga cikin sababbin Musulunta suna boye addininsu saboda gudun a hallaka su, ko kuma tsangwama.”

Wasu mata Musulmai da aka zanta da su a Afikpo da ke Jihar Ebonyi, da Enugu, da Abakaliki, da Umuahia, da Okigwe da Owerri, sun bayyana sunayen cin mutunci da ake kiran su da su da zarar an hange su sanye da hijabi —akan kira mace “dodo” ko “maci amana”.

Mata na ganin tasku

Halima Musa Ani, wata Musulma a Jihar Enugu, ta bayyana yadda aka ci zarafinta a bainar jama’a, har aka yi kokarin tube mata hijabi.

Wasu matan akan kira su da ‘Boko Haram’ ko ‘Bayi’ a duk lokacin da suka shiga motocin haya a garin Afikpo.

Halima ta ce, “Musulmai ’yan kabilar Ibo na fuskantar kalubale sosai a Kudu-maso-Gabas, musamman mata domin ba za mu iya fita ba tare da hijabi ba.

“Da zarar mun fita za su fara kiran mu da ‘Hausawa’, ko karamin yaro da ya hange mu zai fara cewa ga ‘Hausawa’ nan, mun zame musu abun wasa,” inji Halima.

Ta kara da cewa ana danne musu hakkokinsu na ’yan kasa, sannan idan suka je wajen Hausawa neman taimako su ma sai su ce musu ai ba ’yan uwansu ba ne.

Ta ba da labarin yadda zanga-zanga ta barke lokacin da aka kira sunanta, yayin da ta je karbar tallafi.

“Wata mata ta ce me ya sa aka kawo Bahaushiya nan, nan take ta ce na koma jiharmu, saboda ina karyar ni ’yar kabilar Ibo ce.

“Ban yi aune ba na ji sun fara ja min hijabi ta baya, da kyar na samu na tsira a wannan lokacin,” a cewar Halima.

Umar Musa Ani ya shaida mana cewar yawancin mata Musulmai a Jihar Enugu suna canja sunansu saboda gudun fadawa matsala.

Misali, A’isha sai ta koma Asisko, Maryam ta koma Mary Anne.

Wakilcin siyasa

Musulmai ’yan kabilar Ibo sun koka da yadda ba su da wakilci a Majalisar Kasa.

Kwamishina daya tilo gare su a fadin Najeriya, shi ne Suleiman Ukandu, Kwamishinan Kasa da Safiyo  da Tsara Birane na Jihar Abia.

Kazalika, sun koka da yadda ba a koyar da Larabci ko kuma wani darasi da ya shafi addinin Musulunci a makarantu a yankin Kudu-maso-Gabas.

“Mukamin da suke ba wa Musulmai shi ne a Hukumar Jin Dadin Alhazai, wanda ba ya wuce gurbin mutane uku,” a cewar Farfesa Ishaq Akintola, wani mai rajin kare hakkin dan-Adam kuma Darakta Janar na Cibiyar Kare Hakkin Musulmai ta MURIC.

Abubuwa da dama sun sha faruwa a kan Musulmai a yankunan — ko a lokacin zanga-zangar #ENDSARS sai da aka kone masallatai biyu a garin Nssuka na Jihar Enugu.

Babbar Matsala

Wata Musulma a Umuahia, babban birnin Jihar Abiya, da za mu kira Ummi Okoro ta bayyana rashin hadin kan Musulmai a matsayin babbar matsala.

“Babu hadin kai a tsakanin Musulman Ibo, kowa zaman kansa yake yi. Ina ba da misali ne da Jihar Abiya,” inji ta.

‘Ba ma kin Musulmi’

A Jihar Imo kuwa, Nwamkpa Modestus, Babban Mataimaki na Musamman kan Yada Labarai ga Gwamna Hope Uzodinma, ya yi watsi da zargin da ’yan kabilar Ibo Musulmai ke yi na cewar gwamman ya ki jininsu.

“Babu gaskiya kwata-kwata a ce wai ana nuna wa Musulmai wariya a Jihar Imo a karkashin Gwamna Hope Uzodinma…

“Ni dan Jihar Imo ne kuma zan iya ba da tabbacin cewa wannan shi ne karo na farko da na fara jin an ce wai ana nuna wa Musulmi wariya,” a cewarsa.

Bala Ardo, tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Enugu kan lamuran Hadin Kai, ya yi tsokaci a kan lamarin.

“Musulman ’yan kabilar Ibo ’yan asalin Jihar Enugu suna da hurumin neman duk wata dama ba tare da wata tsangwama ko wariya ba.

“Dangane da Gwamnatin Jihar Enugu, akwai dama ga dukkan ’yan asalin jihar, ba tare da nuna bambanci ba.”

A kan zargin nuna wariya da bambanci, Rabaran Emeka Ngwoke, na Sashen Addini da Nazarin Al’adu na Jami’ar Najeriya da ke Nsukka, ya yi tsokaci.

“Babu wani hari, ko hana ’yanci a ko ina a kasar Ibo.

“Akwai wasu ’yan garuruwa a cikin wannan yankin da ke da yawan Musulmai. Suna yin addininsu ba tare da wani cikas ba.”

Shi ma a nasa bangaren, fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya ba da tashi shawarar a kan wannan matsala.

“Hanyar da za ta zama mafita ita ce ’yan kasa su kasance cikin tsari da kare hakkinsu.

“Ya kamata su aika kokensu zuwa ga Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta Kasa, wacce Gwamnatin Tarayya ta kafa don kare hakkin ’yan Najeriya.”

Rabaran Ngwoke ya yi kira da “a kyautata mu’amalar zamantakewa a tsakanin addinai” don samun fahimtar juna yadda ya kamata.

Wakilan gwamnatocin jihohi Enugu da Imo ne kadai suka amsa goron gayyatar tattaunawar da aka bukaci yi da su.