✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’Yan kalare suka kai wa ’yan jarida hari a Gombe

Mutanen gari sun ceci ’yan jairdar daga hannun bata-garin a garin Gombe

A lokacin da harkokin siyasa ke kara kankama, ayyukan ’yan daba da aka fi sani da ’yan kalare a Jihar Gombe, sun dawo, inda bayan rikicin da suke yi a tsakaninsu, suke kai wa jama’ar gari hari.

A wannan karon bata-garin sun yi wa ’yan jarida dirar mikiya, inda a ranar Juma’a wani dan jarida a jihar ya saha da kyar a yayin da suka yi kokarin kwace mishi kyamararsa ta aiki.

’Yan kalaren sun tare dan jaridar da ke aiki da kafar yada labarai ta Gwamnatin Jihar Gombe (GMC), kuma wakilin gidan talbijin na Liberty, Muhammad Ibrahim Pantami, da abokin aikinsa mai daukar masa bidiyo ne a unguwar GRA a cikin babur mai kafa uku, inda suka tsittsinka wa matukin babur din mari.

Bayan sun tsallake rijiya da baya, Muhammad Pantami, ya bayyana cewa, suna cikin tafiya ne suka ci karo da ’yan kalaren, wadanda ya ji suna cewa dan jarida ne su ne masu karantawa a labarai duk sai sun yi maganinsu.

Ana cikin haka, bata-garin suka yi yunkurin kwace masa kyamararsu, amma cikin ikon Allah wasu mutane a mota da za su wuce suka kawo musu dauki.

A cewar Pantami, wanda ke fama da larura a kafarsa da kuma rashin cikakkiyar lafiya, harin bata-garin bai kashe masa gwiwa ba, sai dai ma karin kwarin gwiwar da ya samu na ci gaba da aikinsa.

Game da yadda ’yan kalare ke cin karensu babu babbaka, Pantami ya yi kira ga uwar Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ta dauki matakin da ya dace domin kare mambobinta daga barazanar bata-gari.

Da muka tuntubi Shugaban Kungiyar NUJ Reshen Jihar Gombe, Kwamared Sa’idu Bappah Malala, ya ce za su duba su ga irin matakin da ya dace su dauka wajen shirya tarukan fadakar da ’yan jarida hanyoyin kare kansu daga fadawa tarkon  bata-gari.

Su dai ’yan kalare, idan suka yi zuga suka fito, duk wanda suka samu saran shi suke yi, sannan su kwace duk abin da suka samu a wajen mutanen gari.