✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kallo sun yi wa lafari jina-jina a Ghana

A Lahadin da ta gabata ce wani alkalin wasa a kasar Ghana ya sha da kyar yayin da aka kwato shi daga hannu ’yan kallo…

A Lahadin da ta gabata ce wani alkalin wasa a kasar Ghana ya sha da kyar yayin da aka kwato shi daga hannu ’yan kallo da suka yi masa dukan tsiya yayin wani wasan tamola da ya kasance lafari.

Magoya bayan kungiyar da ya busa wa wasa ne suka fusata da yanayin alkalancinsa inda suka yi masa dukan kawo wuka kamar yadda wani mabiyin shafin Twitter mai suna Fentuo Tahiru Fentuo ya wallafa hotona da bidiyon lamarin.

Lamarin dai ya faru ne yayin da kungiyoyi ’yan matakin farko ke buga wasansu, abin da ya sa aka tashi wasan ke nan tun gabanin lokacin karewarsa.

Rahoton da manema labarai na BBC suka ruwaito a nuna cewa magoya bayan kungiyar Mighty Royal da ke gida ne suka yi wa lafarin bore a wasan da aka buga da kungiyar Tano Bofoakwa wanda suke zarginsa da busa ta rashin adalci.

Alkalin wasan tare da mataimakansa biyu bayan an ceto su

’Yan kallon dai sun yi cincirondo ne a kofar fita ta filin da ake buga wasan, inda daga nan ne suka yunkura ciki su ka yi wa lafarin dukan tsiya, inda har wasu daga cikinsu ke ikirarin sai sun yi masa dukan da zai yi ajalinsa.

A karshe dai ’yan sanda ne suka kwace shi tare da sauran mataimakansan biyu a hannun fustattun ’yan kallo bayan an tara musu gajiya.