✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kannywood sun tara wa Sani SK Naira miliyan Daya

Sani SK ya dade yana fama da cutar suga da ta hanta.

’Yan Kannwyood sun sake tara wa jarumin barkwanci na masana’antar, Sani SK, wanda ya dade yana fama da rashin lafiya kusan Naira miliyan daya domin ya yi jinya, bayan taimakon da suka masa na baya.

Marubuciya ce a masana’antar kuma Shugabar Gidauniyar Creative Helping Needy Foundation, Hajiya Fauziyya D. Suleiman, ce ta bayyana hakan, inda take mayar da martani ga masu turo mata bidiyon jarumin suna cewa a taimaka masa.

A cewarta, “Mutane suna ta turo min wannan bidiyon na Sani SK suna cewa mu taimaka masa; Maganar gaskiya a kwanaki mun yi batun Sani SK a Instagram din nan, kuma wasu daga cikin ’yan fim da mutanen gari sun taimaka masa. Sai dai ciwonsa mai cin kudi ne saboda yana fama da ciwon suga da hanta.”

Fauziyya D. Suleiman ta kara da cewa, “Yanzu haka Abdul Amart Mai Kwashewa ya ba shi Naira dubu 500. Hadiza Gabon ta ba shi Naira dubu 250, Ali Nuhu ya ba shi Naira dubu 100.

“Aliyu Tsamiya ma ta ba shi Naira dubu 100, sannan wasu da yawa ma sun bayar da gudummawarsu daga masana’antar ta Kannywood. Muna addu’a Allah Ya saka musu da alheri.”

Marubuciyar ta kara da cewa ’yan fim din suna kokari matuka, sannan ta yi kira ga mutanen gari da suma su taimaka.

A baya-bayan nan, Sani SK ya fito a fim din Gargada mai dogon zango.