✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Kannywood sun yi tir da hotunan Rahama Sadau

Wasu daga cikin jarumai da sauran masu alaka da harkar fina-finan Hausa ta Kannywood sun bi sahun mutanen da suka yi suka a kan wasu…

Wasu daga cikin jarumai da sauran masu alaka da harkar fina-finan Hausa ta Kannywood sun bi sahun mutanen da suka yi suka a kan wasu hotuna da jaruma Rahama Sadau ta wallafa.

Da dama daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar ta Kannywood dai sun yi tir da jarumar, wasu ma har tsinuwa suka yi, ko dai kai-tsaye, ko kuma a kaikaice.

Jarumar dai ta fito ta nemi afuwa bisa wannan lamari.

A ranar Litinin ne aka wayi gari da hotunan Rahama sanye da wasu tufafi masu nuna jikinta, wadanda suka jawo cece-kuce.

Cece-kuce

Mutane da dama sun yi ta sukar jarumar tare da yin Allah wadai, sannan a gefe daya kuma wasu suka fito suna kare ta.

Jim kadan da musayar yawun ne, sai aka samu bayyanar wani maudu’i mai suna #AssistantAllah, wanda masu kare ta suka fito da shi domin ci gaba da ba ta kariya.

Kazalika, an samu wani wanda har yanzu ba a san ko wane ne ba, da ya yi batanci ga Manzon Allah (S.A.W) a kasan hotunan.

Bayan wannan batancin da aka yi wa Manzon Allah ne Rahama Sadau ta fito ta nesanta kanta da lamarin ta kuma nemi afuwa, inda ta nuna cewa ba da yawunta aka yi batancin ba.

Duk da haka…

Da yake tsokaci a kan lamarin, mawaki Isa Ayagi cewa ya yi, “Hakika mutum yana ba da samfuri ne na tarbiyar da ya samu tun daga yanayin shigarsa. Don haka ba na mamaki ga shigar da jaruma Rahama Sadau ta yi.”

 

HAKIKI MUTUM YANA BADA SAMFURI NE NA TARBIYAR DA YA SAMU TUN DAGA YANAYI SHIGAR SA.DON HAKA BANA MAMAKI GA SHIGAR DA WATA JARUMA @rahamasadau TAYI DOMIN NA KARANTA WANI GURI A SOCIOLOGY INDA AKACE (THE WAY YOU DRESS THE WAY YOU ARE ADDRESS) .YA KAMATA A DINGA TUNANI KAFIN A AIKATA KOWANNE IRIN ABU SABODA GABA KO DOMIN IYALI KO TSUFA KO MUTUWA. MUFA HAUSAWA NE .kuma musulmi ko a india Indai akace jaruma muslims ce shigarta takan zama mai mutumci. kamar su @shrutzhaasan @sanakhan00 @suhanakhan2 @saraalikhan95 all these actress are muslims and they are very religious and respect the dignity of Islam @officialkannywood @kannywood_peace_promoters_tv @tsakar_gida @bbchausa @freedomradiong

A post shared by isah ayagi (@isah_ayagi_) on

Daga nan sai darakta Ali Gumzak ya ce, “Ya ALLAH Ka tsare mu daga musifa da fitinar wannan gurbataccen zamani. Ka saka mu cikin ’yantattun bayinka nagari. Ka tsare mana imaninmu da hankalinmu. Ya Allah Ka karawa Annabi S.A.W salati da salami fil Jannat.”

Shi ma jarumi Sani Danja, wanda ya sanya wani bidiyo da a ciki wani malami ke cewa mutane ne shaidun Allah a ban kasa, ya rubuta cewa, “Allah Ka sa a mana shaida ta alheri a duniya da Lahira.”

 

View this post on Instagram

 

ALLAH KASA AMANA SHAIDA TA ALKAIRI DUNIYA DA LAHIRA AMEEN

A post shared by Sani Musa Danja (@realsanidanja) on

Tsinuwa

Shi kuwa darakta Sheikh Isa Alolo tsinuwa ya yi, inda ya sanya wani hoton rubutu mai dauke da tsinuwa ga Rahama Sadau, sannan ya kara da cewa, “Fada ce ta Manzon Allah S.A.W. ya ce ku tsine musu in kun gansu”.

Fitaccen furodusa, Abdul Amart Mai Kwashewa, cewa ya yi, “Subhanallah! Subhanallah! Subhanallah! Allah mun tuba! Allah mun tuba! Allah mun tuba! Ya Allah kar Ka kama mu da laifukan wawayen cikinmu.”

A kasan rubutun kuma, Sadiya Kabala ta ce, “Amin summa amin.”

 

View this post on Instagram

 

Subhanallah! Subhanallah! Subhanallah! Allah mun tuba! Allah mun tuba! Allah mun tuba! Ya Allah karka ka kamamu da laifukan wawayen cikin mu

A post shared by Abdul Amart Muhammed (@abdulamart_mai_kwashewa) on

Shi ma darakta Sanusi Oscar 442 ya sanya wani hoton rubutu mai dauke da sakon cewa da wanda ya yi, da wanda ya janyo aka yi, Allah Ya tsine musu albarka, sannan ya kara a kasa cewa, “Ni ba ni da kamar masoyina Annabi Muhammadu. Ya fi uwata ya fi ubana ya fi komai nawa. Wanda duk ya taba shi, babu ni babu shi.”

 

View this post on Instagram

 

Ni Banda Kamar Masoyina Annabi Muhammadu’ Yafi Uwata Yafi Ubana Yafi Komai Nawa’ Wanda Duk Yata Bashi Bashi Babu Ni’

A post shared by sunusi_oscar_442 (@sunusi_oscar__442) on

Aminiya ta gano cewa da farko Oscar ya sanya hotunan da suka jawo cece-kucen kafin su janyo batancin, amma daga baya ya cire su.

Tsokacin Ali Nuhu

Ali Nuhu, wanda shi ne asalin uban gidan jarumar, ya wallafa a shafinsa cewa, “Ya Allah Ka sa mu cika da imani. Ka sa mu nisanci duk wani abu da zai zama sanadiyyar jawo mana fushinka. Ya Allah Kai ke yin yadda ka so da bayinka. Allah Ka shirye mu da duk wani wanda yake da niyyar shiryuwa. Ka hane mu taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji. Ya Allah Ka ba mu ikon fahimtar nasiha ko da daga bakin ’ya’yan da muka haifa ne ballantana abokan zama, magabata da abokan sana’a da masoya na gaske albarkacin fiyayyen halitta Muhammad Rasulillah S.A.W. Allah yadda Ka raba mu da iyayenmu lafiya, Ka sa mu gama da duniya lafiya. Mu zama ababen kwantance nagari.”

A kasan rubutun, Abba el-Mustapha da Malam Ibrahim Yala suka amsa suna masu cewa amin.

Shi ma matashin furodusa, Alhaji Khalid Yusuf, wanda aka fi sani da Kherleedo, cewa ya yi, “Na rantse da Ubangijin da ya aiko Annabi Musa da Attaura sai kinga bala’i! Ta dalilinki aka taba wanda Allah Ya fi so, shi kanshi hotan da kika yi masifa ne ga rayuwarki ballantana ta dalilinsa an taba wanda Ya fi matsayi, matsayi.”

Sannan a wani sakon da ya fitar, jaruma Hafsat Idris ta yi magana, inda ta ce, “Gaskiya ne.”

Shi ma jarumi Abdul M. Shareef ya ce, “Tir da hali irin naki, Rahama.”

 

View this post on Instagram

 

Allah ka shiryar damu gaba daya.

A post shared by Abdul M Shareef (@abdulmshareef) on

Alhaji Sheshe cewa ya yi, “Ba na goyon bayan bayyana fasikanci da tozarta addinin Allah ta hanyar bayyana tsiraici. Annabi S.A.W ya ce akwai wasu mutane ’yan wuta ne za su zo nan gaba. Amma ban gansu ba,” In ji manzonmu.
A cikinsu akwai (Kasiyatun Ariyatun) wasu mata da za su rika yin shiga ga kaya a jikinsu, amma kana kallon surar jikinsu kamar tsirara suke. In ji Annabi S.A.W wadannan matan ko kamshin Aljannah ba za su ji ba. Haka Annabi S.A.W ya ci gaba da cewa idan mun gansu mu tsine musu tunda Allah S.W.T Ya tsine musu.”

Shi ma furodusa Abubakar Bashir Maishadda cewa ya yi, “A labarin matan da suka daukaka a Kannywood suka samu kudi wallahi babu ke a tarihinsu. Ba kya amfanar da Kannywood da komai in ban da ki rika jawo mana masifa.

 

View this post on Instagram

 

A labarin Matan da suka DAUKAKA A Kannywood suka samu kudi Wallahi Wallahi babu ke a tarihin su. Bakya amfanar da Kannywood da komai in ban da ki dinga jawo mana masifa. Mu masana’antar nan bamu da abin da ya fita. Amma kullum burin ki shine daga kin jiki shiru, sai kiyi tunanin kalato wata masifar da za’a dinga zancen ki. A tunanin ki hakan shine zai sa a dinga maganar ki. To ina so ki sani duk iskanci ki Akwai wadanda Wallahi Wallahi baki isa kiyi irin iskancin da suka yi ba. Amma yanzu sun zama TARIHI kamar babu su. KIN KUNYATA ADDININ KI A IDON DUNIYA! YAU INA FATI MUHAMMAD FATI BAFFA SAFIYA MUSA ABIDA MUHAMMAD UMMI ZEE ZEE ZAINAB RAGA HADIZA KABARA SADIYA GYALE KUBRA DHAKO ZAINAB INDOMIE LATE RABILU MUSA IBRO LATE AHMED S NUHU LATE USAINA TSIGAI HALISA MUHAMMAD MAIJIDDA ABDULKADIR MAIJIDDA IBRAHIM LATE KULU LATE DAN WANZAN Da sauransu??? Shin a cikin wadannan mutanen dana lissafa akwai wacce ko wanda kika kai DAUKAKA? Yau suna ina? Wasu sun koma ga mahaliccin su! Wasu koma sunyi aure! ANYA KINA TUNANIN ZAMA MAHAIFIYAR WASU? ANYA KINA TUNANIN MAKOMAR ZURI’ARKI KO KUMA AHALIN DA ZAKI HAIFA? Ya Allah Mun TUBA Ya Allah ka shiryi DAN MUSULMI. KIN ZAMA KAICO A ADDININ MUSULUNCI! KIN ZAMA KAICO A WAJEN IYAYENKI! KIN ZAMA KAICO A MASANA’ANTAR KANNYWOOD! KIN ZAMA KAICO A WAJEN AL’UMMAR BAHAUSHE! Muna yi miki fatan shiriya idan ke mai shiriya ce, idan kuma ke ba mai shiriya bace muna rokon Allah ya watsa aniyar ki! WALLAHI DUK MUTUMIN DA YAKE DA MUTUNCI BAZAI AURE KI BA.

A post shared by KING OF KANNYWOOD BOX OFFICE (@realabmaishadda) on

Shi ma Adam A. Zango cewa, “Allah Ka shirye ta idan ta yi taubatan nasuhu. Idan ba mai shiriya ba ce, Allah Ka la’ance ta.”

Shi ma fitaccen daraktan nan kuma jarumi a masana’antar, Falalu Dorayi ya ce yin shiru yayin da aka aikata wata barna, ita ma barna ce.

“Nasiha da jan hankali ba da tozarci ba, ita ce hanya mafi kyau musulmi ya yi wa dan uwansa musulmi nasiha a kan wata barna da ya ga yana aikatawa.

“Ita dai dabi’ar shigar banza nema take ta zama ruwan dare a al’ummarmu.

“Mace tana da daraja ga rayuwarta da ta al’ummarta ne, dan haka mu tashi wajen nusar dasu kunyarsu da mutuncinsu, domin gyara ‘ya’yanmu masu zuwa a gaba”, a cewar Dorayi.

Aminiya ta kuma ci karo da wasu hotunan bidiyo, inda jarumai irinsu Malam Ibrahim Sharukhan suke mata martani.