✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Kannywood wadanda ba jarumai ba da suka rasu

Galibi an fi tuna wadanda ake ganin fuskokinsu a fina-finai.

’Yawancin wadanda suka rasu aka kuma fi tunawa da su a masana’antar Kannywood jarumai ne, sai dai akwai wadanda ba sa fitowa a fina-finai amma sun bayar da gagarumar gudunmawa.

Nura Mustapha Waye wanda ya rasu a kwanan nan, na daya daga cikin wadanda ake tunawa da kuma ambato duk da cewa ba ya fitowa a fina-finai, sai dai irin su ba su da yawa a Kannywood.

Binciken Aminya ya gano cewa, yawancin jaruman ana tunasu da kuma yawan ambatonsu ne a sakamakon wasu shirye-shirye na wasan kwaikwayo da suka fito, kuma haka lamarin yake ga abokan sana’arsu a masana’antar Nollywood da kuma Bollywood

Sai dai a irin wadannan shirye-shirye, a kan manta da wadanda ba a ganin fuskokinsu a fim, duk da kuma sun taka muhimmiyar rawa a masana’antar ta Kannywood.

Ga wasu daga cikinsu:

Nasiru Ishaq Gwale

An fi saninsa da Nasiru dan aljan. Shi ne makadin piyano na farko a Kannywood, wanda kuma ya fara kida a kamfanin Iyan Tama. Marigayin kuma shi ne mai zanen bagon littafan soyayya na kusan duk marubutan da yanzu suka koma rubutun fim.

Balarabe Sango II

Marubuci kuma daya daga cikin dattawan Kannywood da aka kafa ta da su. Ya kuma jagoranci kungiyoyin wasannin kwaikwayo na dabe, ya kuma shugabanci kungiyar masu rubutun fim a zamaninsa.

Auwalu George

Mai daukar hoto da kwalliya, da shirya siddabaru, kuma Darakta ne. Ya rasu ne a shekarar 2017.

Umar Gotip

Mai daukar hoto da kuma haska fitila. Umar Ya rasu bayan rashin lafiya a shekarar 2018.

Dan Azumi Dafe -Dafe

Mai shirin fina-finai da kuma fitowa a wasunsu. Mazaunin Kaduna.

Aminu Mohammed Sabo

Ana masa lakabi da Aminun Sarauniya. Daraktan fina-finan kamfanin Sarauniya da su ka shahara a yin fina-finan gargajiya da na sarauta. Ya rasu a shekarar 2018 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Wadannan sun bayar da babbar gudunmawa a Kannywood. Muna yi musu addu’ar Allah Ya kyautata makwanci.