✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Kasuwar Kantin Kwari 18 da aka sace sun isa gida

Yawancinsu na asibiti saboda dukan da suka sha a hannun masu garkuwar

’Yan Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano 18 da aka yi garkuwa da su a hanyarsu ta zuwa garin Aba domin kasuwanci sun koma ga iyalansu bayan masu garkuwar sun sako su.

Daya daga cikinsu, Abdulkarim Hassan, ya tabbatar wa Aminiya cewa yawancinsu da suka dawo Kano bayan an biya kudin fansa, suna samun kulawa a asibiti saboda dukan da suka sha a hannun masu garkuwar.

“Yau (Lahadi) da safe muka iso Kano bayan an sako mu jiya; muna godiya ga daukacin wadanda suka taya mu da addu’o’i da wadanda suka taimaka aka biya kudin fansar,” inji Abdulkarim.

Sai dai bai yi karin haske game da kudin fansan da aka biya ba domin a sako su.

’Yan kasuwar su 18 sun fada hannun masu garkuwa da mutane ne a garin Okene, Jihar Kogi a yayin da suke hanyarsu ta zuwa fataucin yaduka a garin Aba, Jihar Abiya a ranar Lahadin makon jiya.