✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kasuwar Kantin Kwari sun koka kan dokar Ganduje

A cikin kwamitin da Majalisar Dokokin ta kafa babu mutum daya daga cikin kasuwar.

Kungiyar ’Yan Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano sun roki Majalisar Dokokin Jihar da ta yi la’akari da ’ya’yan kungiyar kafin amincewa da kudurin da ke gabanta a kan kasuwar.

Shugaban Kungiyar, Ambasada Sharif Sagir Wada, ya ce akwai bukatar yin kyakkyawan duba in har da gaske an shirya kawo gyara da sauyi ga matsalolin da suka addabi kasuwar.

Da yake kiran, Wada ya ce kafin tabbatar da dokar, ya kamata a sanya ’Yan Kasuwar Kantin Kwari a cikin kwamitin da aka kafa don magance matsalolinta.

Yayin ganawarsa da manema labarai, Shugaban kasuwar, ya ce a halin yanzu babu wani daga cikin Kasuwar Kwari da aka dauka domin yin wakilci a kwamitin da aka kafa.

A cewarsa, rashin samun wakilcin ’yan kasuwar a kwamitin tamkar an yi tuya an manta da albasa ne, shi ya sa ya ya bukaci Majalisar ta sake nazari kafin ta yanke hukunci.

A kwanakin baya ne Gwamnatin Kano ta aike wa Majalisar Dokokin  Jihar kudurin Kasuwar Kantin Kwari, wanda ya samu karatu na farko.

Kudurin na neman daidaita al’amuran ’yan Kasuwar Kantin Kwari da sauran ’yan kasuwa da ke kasashen waje da kuma na gida.