✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Kasuwar Kwari sun koka kan rashin tsaro a kasuwarsu

‘Yan Kasuwar Tufafi ta Kantin Kwari da ke Kano sun koka kan tabarbarewar tsaro a cikin kasuwar inda hakan ya jefa kasuwar cikin damuwa kan…

‘Yan Kasuwar Tufafi ta Kantin Kwari da ke Kano sun koka kan tabarbarewar tsaro a cikin kasuwar inda hakan ya jefa kasuwar cikin damuwa kan halin da dokiyoyinsu ke ciki.

Alhaji Isa Nuhu daya daga cikin ’yan kasuwar ya alkanta rashin tsaro da kasuwar ke ciki da yawan wuraren shigar kasuwar da ke sa mutane shiga kasuwar a kowane lokaci suka so ba tare da wata ka’ida ba. “A yanzu haka kasuwar ta zama kamar hanyar wucewar mutane saboda yawan mashigu da kasuwar ke da su.  Kowa shiga yake yi lokacin da ya so. A wani lokacin ma a daidai lokacin da mutum yake tashi daga kasuwa a lokacin wadansu suke shigowa, wannan ai ba tsari ba ne,” inji shi.

Malam Jamil Ado da ke sayar da yadi a kasuwar ya shaida wa Aminiya cewa baya ga yawan mashiga da kasuwar ke da su  yanzu haka wadansu ’yan kasuwar sun mayar da ita kamar otel lura da yadda ake shigowa da mata cikin dare ana aikata abin da bai kamata ba.

Ya ce “Za ka ga mata suna shigowa da daddare cikin kasuwar wai sai a fake da cewa kaya za su saya. Wacce macen arziki ce za ta shigo kasuwa da sunan sayayya  da misalin karfe 9 zuwa10 na dare?”

’Yan kasuwar sun yi kira ga shugabannin kasuwar su duba wannan matsala tare da magance ta cikin gagagwa kafin abubuwa su lalace.  “Muna kira ga jagororin kasuwar su kawo mana dauki ko ma samu kwanciyar hankali. Zai yi kyau idan aka tsayar da lokacin shiga da fita daga kasuwar kamar yadda ake yi a sauran kasuwannin  jihar nan,”  inji shi.

Aminiya ta tuntubi Manajan Daraktan Kasuwar, Alhaji Abba Muhammad Bello inda ya ce suna sane da halin rashin tsaro da ake ciki a kasuwar inda ya sha alwashin kawo wa kasuwar gyara nan ba da dadewa ba. “Wannan ofis sabo ne ba mu jima da shigarsa ba, amma yana daga cikin abubuwan da muka fara cin karo da su a kasuwar,” inji shi.

Ya ce, “Kasancewata dan kasuwa lokacin da na zo ni da kaina na zaga kasuwar na ga halin da ake ciki kuma abubuwa ne da ba su yi daidai da tsarin kasuwar ba wanda kuma ba za su haifar wa kasuwar da mai ido ba.

“Za mu dauki matakan gyara ta hanyar da ta dace. Amma abin da za mu fara shi ne mu rage yawan mashigar kasuwar domin haka ne zai sa a samu damar kula da masu shiga da fita. Sannan idan komai ya daidaita za mu dauki matakin sanya lokacin shiga da fita a kasuwar kamar yadda ake yi a sauran kasuwannin jihar nan.

Sanya lokacin da za mu yi zai zama bisa la’akari da lokacin kasuwanci, misali idan ana bude kasuwa da karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, to idan lokacin azumi ya zo wanda ake harkokin Sallah kin ga akwai bukatar a canja lokacin yadda zai taimaka wa ’yan kasuwa da masu sayyaya saboda ganin bakin da ke zuwa kasuwar daga nesa,” inji shi.

Shugaban Kasuwar ya sha alwashin sanya kafar wando daya da duk wanda zai kawo wa kasuwar nakasu a harkokin kasuwanci.“Ba za mu yarda mu zuba ido wadansu baki su zo su kassara kasuwarmu ba. Ba za mu ce ba mu son baki ba, domin ita harkar kasuwanci da bakin ake  yi, mun yarda kowa ya zo ya ci arziki, amma kamata ya yi kowa ya tsaya a matsayinsa. Bakin nan sun hada da na kasashen waje da wadanda ke makwabtaka da mu. Ba za mu yarda wani ya zo ya lalata mana kasuwancinmu ba,” inji shi.

Ya yi wa ’yan kasuwar albishir cewa gwamnatin Jihar Kano tana shirye-shiryen kawo  ayyukan ci gaba a kasuwar inda ya yi kiran su bayar da hadin kai. “Tun kafin zuwanmu Mai girma Gwamna ya fara gyara kasuwar ta hanyar kawo manyan gine-gine a kasuwar wadanda suka kara mata daraja. A yanzu har alfahari mutum yake ya zo da baki ya nuna musu Kasuwar Kwari. Kuma gwamnati tana shirin samar da tituna da magudanun ruwa a cikin kasuwar da wasu karin gine-gine. Kirarmu a ba gwamnati hadin kai wajen tabbatar da abubuwan da za su kawo wa kasuwar ci gaba,” inji Daraktan.