✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kungiyar asiri sun shiga hannu a Edo

Dubunsu ta cika yayin da suka shiga hannun 'yan sandan jihar.

Jami’an ‘yan sanda a Jihar Edo sun cafke wasu mutum biyu a babban birnin Jihar na Benin da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne.

Wadanda ake zargin masu shekara 32 da 24 an cafke su ne a kan titin Benin zuwa Sepele, da ke yankin Etiosa a Jihar.

  1. ’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 28 a Kaduna
  2. A karo na 6, an sake tsawaita wa’adin hada layukan waya da lambar NIN

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta bi sahun wata mota kirar Lexus 330 mai lamba FUG 571 SB wacce ababen zargin suka tuka.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Kongtons Bello wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce an samu bindiga kirar gida guda daya da wasu makamai, sai kuma tabar wiwi da aka samu a tare da su.

A cewarsa, wanda ake zargin sun amsa cewar suna yi wa wata kungiyar asiri da ke birnin Benin aiki ne, inda ya ce za zarar an kammala bincike za a mika su kotu domin yanke musu hukunci.

Kazalika, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, CP Philip Ogbadu ya umarci dukkan kwamandojin yankunan jihar da su sanya ido sosai domin cafke bata-gari a jihar.