✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwadago sun dakatar da yajin aiki

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun dakatar da yajin aiki da zanga-zangar lumana da suka kuduri aniyar farawa ranar Litinin. Wannan mataki ya biyo bayan wata…

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun dakatar da yajin aiki da zanga-zangar lumana da suka kuduri aniyar farawa ranar Litinin.

Wannan mataki ya biyo bayan wata yarjejeniya da aka kulla ne a karshen wata doguwar tattaunawa a tsakanin wakilan kungiyoyin da na Gwamnatin Tarayya.

Wata sanarwar bayan taro da Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya karanta ta ce gwamnati ta amince ta dakatar da karin kudin wutar lantarki da mako biyu har sai wani kwamiti ya yi nazari a kan dacewar sabon tsarin bisa la’akari da hujjojin da aka gabatar na karin.

Sai dai kuma ya ce shirin tsame hannun gwamnati dungurungum daga harkar man fetur na nan daram, yana cewa za a samar da tallafi don rage wa ma’aikata radadin da matakin zai haifar.

“Bayan tattaunawa mai tsawo a kan batutuwan da ’yan Kwadago suka gabatar, Gwamnatin Tarayya ta ce ta tsara wani tallafi da zai sama wa ma’aikatan Najeriya rangwame daga radadin da za su iya fuskanta sakamakon karin kudin wutar lantarki da tsame hannun gwamnati daga harkar samar da man fetur.

“Tallafin zai kasance ne a bangaren sufuri, da wutar lantarki, da samar da gidaje, da noma, da kuma jin kai”, inji sanarwar da Mista Ngige ya karanta.

Sai dai kuma da yake tsokaci a kan lamarin, Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Quadri Olaleye, ya ce an dakatar da yajin aiki da zanga-zangar da mako biyu ne kawai, ba janyewa aka yi ba.

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta cika alkawuran da ta yi kamar yadda aka zayyana a sanarwar bayan taron, yana jan kunne cewa ’yan kwadagon ba za su yi wani gargadi ba za su dauki mataki idan aka samu akasi.

Taron, wanda aka fara da kusan karfe 8.30 na daren Lahadi aka kuma kai talatainin dare ana yi, ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi Chris Ngige, da Minista a Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyukan Yi Festus Keyamo, da Minista a Ma’aikatar Samar da Wutar Lantarki Godwin Jeddy-Agba, da kuma Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) Mele Kyari.