✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Najeriya 10 da suka lashe kofi a Turai a bana

Ba a taba samun shekarar da ’yan Najeriya suka lashe kofuna a Turai ba kamar bana.

A daidai lokacin da ake kare gasannin kwallon kafa a kasashen Turai da kasashe da dama sun kammala wasu ke dab da kammalawa, hankali ya koma ne kan wadanda suka lashe kofuna ko kungiyoyin da suka samu nasarar shiga manyan gasanni na nahiya ko kuma kungiyoyin da za su koma kananan gasanni.

Binciken Aminiya ya gano cewa an dade ko ma ba a taba samun shekarar da ’yan kwallon Najeriya suka lashe kofuna a Turai ba kamar bana.

Baya ga kofuna da ’yan Najeriya suka lashe da yawansu bana sun haska a kasashe da suka taka leda.

Aminiya ta rairayo ’yan kwallo 10 da suka lashe kofuna a bana kamar haka.

Kelechi Iheanacho da Wilfred Ndidi: Kofin Kalubale na Ingila

Ndidi da Iheanacho rike da tutar Najeriya bayan sun lashe
Gasar FA Cup ta Ingila

Iheanacho da Ndidi ’yan wasan Kungiyar Leicester City ta Ingila ce. Kungiyar ce ta lashe Kofin Kalubale wato FA Cup na Ingila, inda ta lallasa Kungiyar Chelsea da ci daya mai ban haushi a wasan karshe.

A wasan wanda aka buga a ranar 15 ga Mayun bana, an fara da ’yan wasan Najeriya guda biyu sannan dan wasan kungiyar, Youri Tielemans ne ya zura kwallo daya tal a ragar Chelsea.

Ndidi yana cikin zaratan ’yan wasan Kungiyar Leicester City, inda da wahala a cire zaratan ’yan wasan biyar ba a kira sunansa ba.

A bangaren, Iheanacho kuwa, kakar bana ce kakar da ya fi haskawa, inda a bana ya zura kwallo 19, wanda hakan ya sa ya zama dan wasan kungiyar da ya fi zura kwallo a bana, sama da Jammy Vardy.

Kafin kakar bana, Iheanacho ya taba kwashe shekara daya cur bai zura kwallo ba, sannan akwai kakar da ya zura kwallo biyu kawai, wanda hakan ya sa magoya bayan kungiyar suka fara tunanin sun yi asarar kudinsu ne.

Samuel Chukwueze: Kofin EUROPA

Chukwueze rike da Kofin Europa

Dan wasan gaba na Najeriyar ya lashe gasar Europa League ta bana da Kungiyar Villareal wadda ta doke Manchester United a wasan karshe.

Dan wasan wanda jinyar rauni ta hana shi buga wasan na karshe, ya zura kwallo daya a wasa 11 na gasar ta Europa, sannan ya taimaka aka zura kwallo hudu.

Ya samu rauni ne a wasan gasar ta kusa da karshe tsakaninsu da Arsenal A kakar bana baki daya, ya zura kwallo hudu sannan ya taimaka an zura kwallo shida.

Tuni aka yi wa dan wasan tiyata a kafarsa ta hagu, aikin da kungiyar ta fitar da sanarwar cewa an yi nasara.

Joel Aribo da Leon Balogun: Firimiyar Scotland

A kasar Scotland, ’yan wasan Najeriya guda biyu: Joel Aribo dan wasan tsakiya da Leon Balogun, dan wasan baya sun lashe gasar Firimiyar Scotland ce da Kungiyar Rangers.

A kakar ta bana, dan wasan tsakiyan Joel Aribo ya zura kwallo shida a wasa 25 da ya buga sannan ya taimaka aka zura kwallo hudu.

Shi ma Balogun ya nuna kwarewa matuka.

Asisat Oshoala: Kofi uku a Spain

Asisat Oshoala da kofunan da ta lashe a bana

’Yar wasan Najeriya, Asisat Oshoala ta lashe kofi uku da Kungiyar Barcelona ta mata a kakar bana.

Ta lashe firimiya ta mata ta Spain wato Spanish Primera Iberdrola da Spanish de la Reina da kuma gasar Zakarun Turai ta mata wato UEFA Women’s Champions League.

A kakar bana, ta zura kwallo 13, sannan ta taimaka an zura kwallo biyu duk da cewa ta sha fama da jinya a bana.

Peter Olayinka: Kofin Czech

Dan wasan gaba na Najeriya ya lashe kofi biyu da Kungiyar Slavia Prague: Gasar Firimiyar Czech da Kofin Czech.

Dan wasan yana cikin zaratan ’yan wasan kungiyar, inda ya zura kwallo 11 sannan ya taimaka aka zura kwallo 5 duk da shi ma ya sha fama da jinya a kakar ta bana.

Paul Onuacha da Cyriel Dessers

Dan wasan gaba na Najeriya, wanda yanzu tauraronsa ya fi haskawa, Paul Onuachu da takwaransa Cyriel sun lashe gasar Kofin Beljiyum ta bana da Kungiyar Genk.

A bana Onuachu ya zura kwallo 33 a wasa 38.

Shehu Abdullahi: Kofi daya a Cyprus

Shehu Abdullahi rike da kofin da suka lashe

Dan wasan baya na Najeriya, Shehu Abdullahi ya lashe gasar Firimiyar Cyprus da Kungiyar Omnia Nicosia.

Dan wasan ya koma kungiyar ce a farkon kakar bana daga Kungiyar Bursaspor ta Turkiyya, inda za a iya cewa ya fara da sa’a, kuma ya shiga cikin zaratan ’yan wasan kungiyar.