✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Najeriya da suke haskawa a kasashen waje

Najeriya ta yi fice matuka wajen fitar da zaratan ’yan wasan kwallon kafa a duniya ba ma a Afirka kadai ba. A wata kididdiga besoccer.com ta…

Najeriya ta yi fice matuka wajen fitar da zaratan ’yan wasan kwallon kafa a duniya ba ma a Afirka kadai ba.

A wata kididdiga besoccer.com ta yi, ta ce Najeriya ce kasa ta 8 a duniya da ta fi yawan ’yan kwallon a duniya, kuma ta daya a Nahiyar Afirka.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna, a kasar Ingila, inda ake kallo a matsayin duniyar kwallon kafar, akwai ’yan wasan kwallon kafan Najeriya 35 da suke taka leda.

A kasar Spain kuwa, akwai ’yan Najeriya 29, sai Italiya, inda ’yan kwallon Najeriya 10 ke taka leda, sai Jamus guda 18, Faransa guda 7.

A cikin kasashen da akwai ’yan wasan Najeriya, Portugal ce ke kan gaba, ’yan kwallon Najeriya guda 74 da suke taka leda a kasar.

Daga cikin wadannan ’yan wasan akwai wadanda tauraronsu ke haskawa, akwai ’yan tsaka-tsakiya, sannan akwai masu zaman kashe wando a benci.

Wannan ya sa Aminiya ta lalubo wasu daga cikin wadanda a bana suka fi haskawa.

Zaidu Sanusi

Zaidu Sanusi haifaffen garin Jega a Jihar Kebbi a Arewacin Najeriya, a yanzu haka yana buga lamba 3 a kungiyar FC Porto ta kasar Portugal.

A kakar 2021 ce Porto ta sayo Zaidu daga kungiyar Santa Clara ta Portugal din ita ma, kuma tun zuwansa likafarsa ke kara gaba.

A makon jiya ya jagoranci FC Porto wajen fitar da kungiyar Jubentus daga gasar Zakarun Turai, inda ya sha fama da ’yan wasan gaban Jubentus, ciki har da Cristiano Ronaldo.

Ya lashe kofin Super Cup na Portugal, inda suka doke Benfica da ci 5 – 0.

Kusan duk wasannan kungiyar yana zura kwallo.

Wasa daya ya buga wa Najeriya, a wasan da Algeria ta lallasa Najeriya da ci daya da nema a watan Oktoban bara.

Joe Aribo

Joseph Oluwaseyi Temitope Ayodele-Aribo, wanda aka fi sani da Joe Aribo dan wasan tsakiyan kungiyar Rangers ce ta Scotland.

A makon jiya ne Joe Aribo da kungiyarsa ta Rangers suka lashe gasar Firimiyar Scotland bayan shekara 10 suna nema, duk da cewa saura wasa 10 a kammala gasar.

A kakar ta bana, Aribo ya guda wasanni 52, sannan ya zura kwallo 9.

Joe Aribo ya buga wa Najeriya wasa 6, sannan ya zura kwallo 2.

Paul Onuachu

A yanzu haka ya fi kowane dan kwallo zura kwallaye a raga, inda ya zura kwallo 26 a kakar bana.

Ya buga wa Najeriya wasa 9, ya kuma zura kwallo 1.

 

Leon Balogun

A kungiyar Rangers din kuma akwai dan wasan bayan Najeriya, Leon Balogun, wanda shi ma ya buga wasa 17 a kakar bana da suka lashe gasar.

Balogun, za a iya cewa ya je Rangers da kafar dama, bayan dogon lokaci da ya dauka yana fafutuka a kungiyoyin Firimiyar Ingila, inda a lokuta da dama zaman benci yake yi.

Balogun ya buga wa Najeriya wasa 32, ciki har da gasar Kofin Afirka ta karshe da Najeriya ta je.

Wildred Ndidi

Onyinye Wilfred Ndidi, dan wasan tsakiyan Najeriya ne da ke taka leda a kungiyar Leicester City ta Ingila.

Dan wasan ya yi fice matuka a gasar Firimiyar Ingila, inda a lokuta da dama yake kasancewa dan wasan tsakaiyan da ya fi kwato kwallo a kafar abokan karawa.

 

Maduka Okoye

Maduka Emilio Okoye, golan Najeriya ne da ke tsaron gidan kungiyar Sparta Rotterdam ta kasar Holland.

Zuwa yanzu, Okoye ya kama wasa akalla biyar da ba a zura masa kwallo a ragarsa ba.

A wasan da Najeriya ta yi kunnen doki da Brazil a Oktoban bara ne ya fara tsare gidan Najeriya.

 

Simon Moses

Moses Daddy-Ajala Simon, dan wasan Najeriya ne da ke taka leda a kungiyar FC Nantes ta kasar Faransa.

Kusan dukkan wasannin Nantes yana ciki, kuma a kakar bana ya zura kwallo biyu.

Ya buga wa Najeriya wasa 3, inda ya zura kwallo 5.

Sadik Umar

Umar Sadik, dan wasan Najeriya ne da ke taka leda a kungiyar UD Almeria ta kasar Spain.

A yanzu shi ne yake jagorantar gaban kungiyar, inda ya zura kwallo 14.

Sadik yana cikin ’yan wasan da suka lashe tagulla a gasar Olympic ta shekarar 2016, inda ya zura kwallo hudu.

Yanzu kocin Najeriya ya sake kiran shi domin ya buga wasan Najeriya na gaba.

Sauran wadanda suka yi kokari sun hada da Kenneth Omerua na kungiyar Leganes ta Spain, da Aled Iwobi na Eberton da Samuel Chukwueze na Billareal.