✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Majalisar Kebbi 6 sun yi murabus

Babu cikakken bayani kan dalilin 'yan majalisar na yin murabus din.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Usman, da wasu mambobin majalisar biyar sun yi murabus a ranar Alhamis.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wasikar da Sakataren Majalisar, Shehu Muhammad-Yauri, ya rattaba wa hannu wadda aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

“Manyan jami’an Majalisar shida, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar sun yi murabus daga mukamansu,” in ji wasikar.

Wasikar ta nuna 20 daga cikin mambobi 24 da majalisar ke da su suka sanya hannu a wasikar ajiye mukamamn takwarorin nasu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa babu wani cikakken bayani kan dalilin yin murabus din da jami’an suka yi.

(NAN)