✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Majalisar Wakilai 4 na Zamfara sun koma APC

Sun alakanta sauyin shekar da rikicin da ya mamaye PDP a Jihar Zamfara.

’Yan Majalisar Wakilai hudu daga Jihar Zamfara sun sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki a kasar.

An sanar da sauyin shekar ta su ce cikin wata wasika mai dauke da sa hannu Suleiman Ahmed Gummi, wacce aka karanta yayin zaman majalisar na ranar Talata.

’Yan Majalisar da suka koma APC sun hada da Bello Hassan Shinkafi, Ahmed Bakura, Ahmed Shehu da Suleiman Ahmed Gummi.

A cikin wasikar, ’yan majalisar sun ce komawarsu jam’iyyar APC na da alaka ne da rikicin cikin gida da ya mamaye jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara.

Sun ce a dalilin rikicin ne ya sanya Uwar jam’iyyar ta kasa ta dauki matakin sauke dukkanin shugabanninta na jihar.

A karshen watan Yunin da ya gabata ne Gwamna Muhammad Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Biyo bayan komarwarsa ce ’yan majalisar tarayya da na dokokin jihar ke ci gaba tururuwar bin sahun gwamnan wajen sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.