’Yan Najeriya 30,000 ke mutuwa a shekara saboda shan sigari —WHO | Aminiya

’Yan Najeriya 30,000 ke mutuwa a shekara saboda shan sigari —WHO

Zanen Illar Shan Sigari
Zanen Illar Shan Sigari
    Ojoma Akor, Rahima Shehu Dokaji

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce fiye da ’yan Najeriya 30,000 ne ke mutuwa duk shekara a sanadiyar cututtukan da ke da alaka da shan taba sigari.

WHO ta bakin wakilinta Walter Mulombo ta bayyana cewa adadin ya ninka na mutum 3,144 da cutar COVID-19 ta kashe a Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin kaddamar da manhajar adana bayanan tsare-tsaren yaki da shan sigarin A Najeriya, wadda Kamfanin IREX  da hadin guiwar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya suka samar, a bikin Ranar Yaki da Shan Sigari ta Duniya, ranar Talata.

A nasa bangaren, Ministan Lafiya, Adeleke Mamora, ya ja hankalain ’yan Najeriya da su guji shan sigari ko zama a inda ake sha, domin hakan ya fi illa ga lafiyar jikin dan Adam kamar yadda masana kiwon lafiya ke fada.

Minitsan ya kuma ce tun daga ranar 1-6-2022, Najeriya ta fara amfani da sabon tsarin biyan harajin taba sigari na shekara uku da zai kare a shekara ta 2024.