✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya 7 da ke wakiltar wasu kasashen a Gasar Kofin Duniya

Bana Najeriya ba ta samu halartar gasar ba, wanda ya sa wasu magoya bayanta ba su ma cika damuwa da gasar ba, wasu kuma ke…

A ranar 20 ga watan Nuwamban bana ce aka fara fafata Gasar Cin Kofin Duniya ta bana a kasar Qatar.

Sai dai a wannan karon, Najeriya ba ta samu halartar gasar ba, wanda hakan ya sa wasu magoya bayan kasar ba su ma cika damuwa da gasar ba, yayin da wasu kuma suke nuna kaunar wasu kasashen Afirka.

Aminiya ta rairayo wasu ’yan wasa ’yan asalin Najeriya da suke buga wa wasu kasashe wasa a gasar da ake ci gaba da fafatawa.

1- Jamal Musiala

Jamal Musiala dan wasan kasar Jamus ne da asalin dan Najeriya. An haife shi ne a Jamus, amma mahaifinsa dan Najeriya ne, mahaifyarsa kuma ’yar Jamus ce.

Ya taso ne a Ingila sannan a yanzu yana buga kwallo a kungiyar Bayern Munich.

Musiala hoto daga livescore.com

2- Bukayo Saka

Bukayo Ayoyinka Saka, an haife shi a Landan ne, amma duk mahaifiansa biyu, Adenike da Yomi, Yarbawa ne.

Yanzu haka dan kwallon yana buga wa kungiyar Arsenal wasa ne. Sannan yana cikin ’yan wasan tawagar Ingila a gasar ta bana.

Bukayo Saka. (Hoto: arsenal.com)

3- Karim Adeyemi

Karim David Adeyemi,  dan wasan kasar Jamus ne da ke taka leda a kungiyar Dortmund ta kasar.

An haifi Karim a Najeriya ne a shekarar 2002 kuma mahaifinsa dan Najeriya ne, amma mahaifiyarsa ’yar Romania ce.

Karim ya girma a Jamus, sannan yana cikin tawagar ’yawan kasar Jamus a gasar ta bana.

4- Samuel Adekugbe

Shi kuma Samuel Ayomide Adekugbe yana wakiltar kasar Canada ce a gasar ta bana, amma asalinsa dan Najeriya ne.

A Landan aka haife shi, amma iyayensa asalinsu ’yan Najeriya ne mazauna Ingila, wadanda suka koma Canada tun yana dan shekara 10.

5- Ike Ugbo

Iké Dominique Ugbo shi ma kasar Canada yake wakilta a gasar ta bana, duk da cewa a Ingila aka haife shi.

Amma iyayensa wadanda asalinsu ’yan Najeriya ne sun koma Canada ne tun yana dan shekara biyar.

6- Manuel Akanji

Manuel Obafemi Akanji dan wasan kasar Switzerland ne amma asalinsa dan Najeriya ne.

An haife shi ne a birnin Neftenbach na kasar Switzerland, kasar mahaifiyarsa, amma mahaifiansa dan Najeriya ne.

7- Noah Okafor

Noah Arinzechukwu Okafor shi ma asalin dan Najeriya ne da ke wakiltar kasar Switzerland a gasar ta bana.

An haife shi a birnin Binningen na kasar.

Mahaifinsa dan Najeriya ne, amma mahaifiyarsa ’yar kasar Switzerland ce.