✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan Najeriya da suka zama zakarun gwajin-dafi a Duniya

Akwai ’yan Najeriya da dama da ke ci gaba da daga martabar kasar a duniya a sakamakon wasu madafan iko da suka rika ko kuma…

Akwai ’yan Najeriya da dama da ke ci gaba da daga martabar kasar a duniya a sakamakon wasu madafan iko da suka rika ko kuma wata muhimmiyar rawar gani da suke takawa a fannoni daban-daban na inganta rayuwa da ci gaban al’umma.

Aminiya ta kawo muku kadan daga cikin mafi shura na ire-iren mutanen Najeriya da suka zama zakaran gwajin dafi a duniya.

  • Ngozi Okonja-Iweala
Ngozi Okonja-Iweala

A ranar Litinin ne aka tabbatar da Ngozi Okonja-Iweala, a matsayin Shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya

Tsohuwar Ministar Kudin ta Najeriya, ta zama mace kuma ’yar Afirka ta farko da za ta shugabanci Kungiyar Kasuwancin ta Duniya.

Okonjo-Iweala ta zubar da manyan ’yan takara takwas wajen samun wannan mukami da aka dade ana ja-in-ja wajen samun wannan mukami a yayin da tsohuwar gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta juya mata baya.

Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da tauraruwarta za ta haskaka a idon duniya ba, inda ta rike mukamai da dama ciki har da mukami na biyu mafi girma daga shekarar 2007 zuwa 2011 a tsawon shekara 25 da ta shafe a Bankin Duniya.

Ta kuma yi aiki a Bankin Ci gaban Afrika (AfDB) da Asusun Bayar da Lamuni da kuma Bankin Zuba Hannun Jari na Asiya (AIIB).

Har a yanzu Okonja-Iweala mamba ce a kwamitin gudanarwar Bankin Standard Chartered sannan kuma ta taba zama mamba a Cibiyar Kawancen Duniya kan Rigakafi (GAVI) a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

  • Akinwumi Adesina
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina

Adesina mai shekaru 61 da ke zaman tsohon Ministan Noma da Raya Karkara a Najeriya, shi ne Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika (AfDB).

A shekarar 2015 ce Adesina ya zama dan Najeriya na farko da ya fara rike shugabancin wannan bankin da ke zama na biyar a jerin manyan cibiyoyin kudi na duniya masu bayar da bashi.

Kafin nadinsa a matsayin Minista a shekarar 2010, Adesine shi ne Mataimakin Shugaban Sashen Tsare-Tsare na Cibiyar Kawancen Afrika ta Green Revolution.

A watan Agustan bara ce aka sake zaben Mista Akinwumi Adesina a matsayin wanda zai ci gaba da jagorantar bankin a wani sabon wa’adi na biyu mai shekaru biyar.

Tamkar Okonja-Iweala, Adesina ya fuskanci tangarda daga gwamnatin tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, a yayin da yake sake neman shugabancin Bankin a wa’adi na biyu, inda aka rika shigar da bukatar bincikarsa kan zargin rashawa duk da kwamitin tabbatar da da’ar ma’aikatan bankin ya wanke shi.

  • Amina Mohammed
Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed

Amina Mohammed ’yar Najeriya ce kuma kwararriya a kan harkokin siyasa da diflomasiyya, wacce a yanzu ita ce cikon ta biyar cikin jerin mutanen da suka rike mukamin Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar 24 ga watan Fabrairun 2017 ne Amina ta yi ajiye mukaminta na Ministar Mahalli domin karbar mukamin Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, mukamin da har yanzu take kai.

Daga shekarar 1981 zuwa 1991, Amina Mohammed ta yi aiki a Archon Nigeria-Norman da kuma aiki da Dawbarn United Kingdom a shekarar 1991. Ta kuma samu nasarar kafa Kamfanin Afri-Project Consortium, daga shekarar 1991 zuwa 2001.

A tsakanin shekarar 2002 zuwa 2006 ne ta kasance mai gudanar da gangamin wayar da kai kan jinsi da ilmantarwa a karkashin shirin cimma muradin karni a Majalisar Dinkin Duniya.

Daga bisani ta zama babbar mai taimakawa Shugaban Kasar Najeriya kan shirin cimma muradin karni na Millenium Development Goals (MDG’s).

Kazalika, Amina mai shekaru 59, ta taba rike mukamin mai bayar da shawara ta musamman ga tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon, kan tsare-tsaren ci gaba a shekarar 2015.